Kun zabeni, kun karrama ni - Biden ya daukar wa Amurkawa muhimmin alkawari
- Zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya mika sakon godiyarsa ga daukacin jama'ar kasar
- Ya ce ya gode da damar da suka bashi na mulkar kasar mai daraja, tuni gidajen talabijin suka fara bayyana nasararsa
- Ya samu nasarar doke Donald Trump da kuri'un kwalejin zabe 284, inda ya zama shugaban kasar na 46
Zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya mika sakon godiyarsa ga daukacin 'yan kasar Amurka saboda zabensa da suka yi don ya mulki kasar.
Biden mai cike da farinciki yayi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya ce zai mulki kowa cikin adalci, The Punch ta wallafa.
Kamar yadda ya wallafa, "Jama'an kasar Amurka, ina mai farinciki da ku ka bani damar mulkar wannan kasa mai daraja.
"Duk da muna da babban aiki a gabanmu, amma nayi alkawari zan mulki kowa bisa adalci- da wadanda suka zabeni da wadanda ba su zabe ni ba.
"Zan tabbatar na yi aiki tukuru, kamar yadda ku ka amince da ni."
Manya-manyan gidajen talabijin da ke ciki da wajen Amurka suna ta nuna yadda Biden ya kayar da Donald Trump.
Gidajen talabijin kamar CNN, NBC, Al Jazeera da sauran gidajen talabijin sun yi ta taya sa farinciki.
Kamar yadda labarai suka yi ta yawo, Biden ya kayar da Trump da kuri'un kwalejin zabe 284, inda yayi nasarar zama shugaban kasar Amurka na 46.
Biden mai shekaru 77, shine mafi tsufa a shugabannin kasar Amurka da aka taba zaba. Trump mai shekaru 74 kuwa ya zargi magudi a zaben.
Dama Biden ya yi shekaru 8 a matsayin mataimakin shugaban kasa Barack Obama. Ya samu nasarar ne bayan ya nemi mulkin a karo na uku.
KU KARANTA: Taron ASUU da FG: An tashi dutse a hannun riga, za a cigaba da yajin aiki
KU KARANTA: Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci
A wani labari na daban, a jiya ne CNG ta kushe taron da NGF suka yi a Kaduna, ta ce maimakon taron ya karkata matsalolin arewa kamar harkokin tsaro, rikicikin matasa, rashin ayyukan yi, talauci, harkar noma da tabarbarewar tattalin arziki, sai ya karkata a kan kananun matsaloli.
A wani taro da CNG tayi jiya a Kaduna, ta ce maimakon NGF ta mayar da hankali a kan manyan matsaloli, sai suka karkata a kan rikicin EndSARS da kuma matsalolin kafafen sada zumuntar zamani wanda hakan ba itace babbar matsalar arewa ba a yanzu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng