Sojoji sun tarairaya masu zanga-zanga, har ruwa da lemu suka raba a Lekki tollgate - Kwamanda

Sojoji sun tarairaya masu zanga-zanga, har ruwa da lemu suka raba a Lekki tollgate - Kwamanda

- Kwamandan bataliya ta 65, Salisu Bello, ya musanta kashe-kashen da sojoji suka yi a Lekki Tollgate

- A cewarsa, har ruwa da ruwan lemu sojoji suka gabatar wa da masu zanga- zangar EndSARS don Karamci

- Sannan duk karar harbi da aka ji a Lekki, sojoji sun yi ne a sama ne don tsoratar da masu zanga-zangar

Masu zanga-zangar EndSARS sun kai wa sojoji hari a Lekki Toll gate ranar 20 ga watan Oktoba 2020, cewar Salisu Bello, kwamandan bataliya ta 65 ta sojoji.

Kamar yadda PUNCH ta ruwaito, Bello yayi ikirarin hakan a wata takarda da ya gabatar wa kotu dangane da harbe-harben da aka yi a Lekki.

Gwamnatin jihar Legas ta samar da wata kwamitin da za ta yi bincike tukuru a kan kashe-kashen, inda take tunanin hakan ne zai kawo zaman lafiya a jihar.

Bello, wanda ya musanta kashe-kashen da aka alakanta da sojoji a Lekki toll gate ya ce masu zanga-zangar sun yi farincikin ganinsu.

Kwamandan sojin ya kara da cewa, har ruwa da ruwan lemu suka mika wa masu zanga-zangar, suna masu rokon su da subar wurin, su koma gidajensu.

A cewarsa, yayin da ya tunkari babban titin Lekki-Ajah wuraren 6:45 na yamma, ya ji karar harbe-harbe wuraren tollgate, ya hango masu zanga-zangar lumanar a hargitse.

Yana isa wurin ya fara rokon jama'an da su koma gidajensu gwamnatin jihar ta sanya kullen awanni 24, kawai sai jama'a suka kwashi duwatsu, kwalabe da sauran miyagun makamai suna jifam sojoji, har su na kona tayoyi, a cewarsa.

A cewarsa, "Har harbi na yi a sama, don in tsoratar da su. Amma wasu daga cikin masu zanga-zangar da na bai wa ruwan lemu da ruwa don su tafi, suka cigaba da zama a bakin gate din."

Ya ce harbin da sojoji suka yi, a sama suka yi. Sannan ya musanta kashe-kashe da boye gawawwaki da mutane suka yi ta ikirari sojoji sun yi.

KU KARANTA: Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

Sojoji sun tarairaya masu zanga-zanga, har ruwa da lemu suka raba a Lekki tollgate - Kwamanda
Sojoji sun tarairaya masu zanga-zanga, har ruwa da lemu suka raba a Lekki tollgate - Kwamanda. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kun zabeni, kun karrama ni - Biden ya daukar wa Amurkawa muhimmin alkawari

A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel