Hoton abinda aka ga Trump yana yi bayan shan mugun kaye a hannun Biden

Hoton abinda aka ga Trump yana yi bayan shan mugun kaye a hannun Biden

- Ga dukkan alamu Donald Trump bai damu ba da shan mummunan kaye da Joe Biden yayi masa ba

- Dama an sanar da nasarar Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka, wanda yafi samun dunbin kuru'u

- An yita cece-kuce bayan ganin Trump yana wasan kwallon golf, inda wasu ke cewa sun lura ko a jikinsa

An hango Donald Trump bayan sanar da nasarar Joe Biden, yana wasan kwallon golf. An hango Trump sanye da wata farar hula, riga mai nauyi, wata riga da kuma takalminsa.

An sanar da nasarar Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka na 46 amma Trump bai nuna damuwarsa ba.

Dama Trump yana son wasan golf tun bayan hawansa karagar mulki, inda yace ya gaji shugaban kasa Barack Obama ne, wanda shima yake yawan yin irin wasan.

Yadda aka san Trump da nuna adawarsa ga Biden karara, an yi matukar tunanin za a gansa a mawuyacin hali, amma sai aka ga akasin hakan.

KU KARANTA: Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

Hoton abinda aka ga Trump yana yi bayan shan mugun kaye a hannun Biden
Hoton abinda aka ga Trump yana yi bayan shan mugun kaye a hannun Biden. Hoto daga by Scot Olson and Evan Vucci
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 5, sun ceto mata 3 da yara a Katsina

A wani labari na daban, zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya mika sakon godiyarsa ga daukacin 'yan kasar Amurka saboda zabensa da suka yi don ya mulki kasar.

Biden mai cike da farinciki yayi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya ce zai mulki kowa cikin adalci, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda ya wallafa, "Jama'an kasar Amurka, ina mai farinciki da ku ka bani damar mulkar wannan kasa mai daraja.

"Duk da muna da babban aiki a gabanmu, amma nayi alkawari zan mulki kowa bisa adalci- da wadanda suka zabeni da wadanda ba su zabe ni ba.

"Zan tabbatar na yi aiki tukuru, kamar yadda ku ka amince da ni."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng