Da tsatsaurin ra'ayin Musulunci muke yaki, ba da addinin Musulunci ba - Shugaban kasar Faransa, Macron

Da tsatsaurin ra'ayin Musulunci muke yaki, ba da addinin Musulunci ba - Shugaban kasar Faransa, Macron

- Shugaban kasar Faransa ya yi amai ya lashe, ya ce ba da addinin Musulunci yake yaki ba

- Macron ya ce an fara karantar da yara kin jinin kasar Faransa a makantu shiyasa ya zabura

- Ya karyata zargin cewa yana kyaman Musulmai kuma yana kwadaitar da mutane kyamatansu

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na yaki da tsatsaurin ra'ayin Musulunci ne, amma ba da addinin Islama ba.

Macron ya bayyana hakan ne yayinda yake martani kan labarin da kamfanin jaridar Financial Times ya wallafa inda yace an yi masa mumunan fahimta kuma daga baya an cire labarin da shafin yanar gizon jaridar.

A wasikar da ya aikewa Editan Jaridar ranar Laraba, Macron yace Financial Times ta tuhumeshi da "kyaman Musulman kasar Faransa don manufa ta siyasa kuma yana ingiza mutane don nuna musu kiyayya."

Amma Macron ya musanta haka inda yace lallai akwai masu kokarin shuka ta'addanci a kasar Faransa amma ba wai yana yaki da Musulunci bane.

"Ba zan bari kowa ya ce Faransa, ko gwamnatinta, na yada wariya ga Musulmai ba, " yace.

"A wasu unguwanni da kuma yanar gizo, wasu kungiyoyin da ke da alaka da masu tsatsaurin ra'ayi suna koyar da kiyayyan jamhuriyyarmu ga yaranmu, suna fada musu su daina bin dokokin kasa,"

"Abinda take yaki da shi kenan....kiyayya da kuma kashe-kashe dake barazana ga yaranta - amma ba addinin Islama ba. Bamu yadda da yaudara ba, tsatsaurin ra'ayi da ta'addanci ba. Ba addini ba."(Economic Times)

Da tsatsaurin ra'ayin Musulunci muke yaki, ba da addinin Musulunci ba - Shugaban kasar Faransa, Macron
Da tsatsaurin ra'ayin Musulunci muke yaki, ba da addinin Musulunci ba - Shugaban kasar Faransa, Macron
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya yi kalaman da suka haifar da zanga-zanga a kasashen Musulmai watan da ya gabata bayan kisan wani malamin makarantar da yayi zanen isgili ga Manzon Allah (SAW)

Yace kasar Faransa ba za ta daina bari mutane na zanen batanci ga manzon Allah ba.

Sakamakon yanke alaka da kuma nisantan kayayyakin Faransa da akayi a duniya, Macron ya bayyanawa Al-Jazeera cewa gaskiya ya fahimta zanen ka iya batawa wasu rai. (Daily Trust)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng