Yanzu-yanzu: Hukumar yan sanda ta sammaci Rahama Sadau, bayan hotunanta sun haddasa kalaman batanci
- Duk da bidiyo da hirar da tayi, ana tsoron kalaman batanci da hotunan Rahada Sadau ya haifar ka iya haddasa fitina
- Tsoron haka IGP Adamu ya bada umurnin gudanar da bincike cikin gaggawa
Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin gudanar da bincike kan 'yar wasar dirama, Rahama Sadau, kan cece-kucen da ya biyo bayan hotunan tsiraicin da ta wallafa kan dandalin sada zumunta.
'Yar wasan diraman ta daura wasu hotuna kuma hakan ya haddasa kalaman batanci ga manzon Allah (SAW).
Daga baya Rahama ta bada hakuri kuma ta goge hotunan da ta daura. Hakazalika ta barranta kanta da kalaman batancin.
Mujjarlar wasar kwaikwayon Kannywood, Mujallar FIM, a ranar Asabar ta ruwaito cewa 'yar wasan ta dakatad da tafiya birnin Dubai da ta shirya yi domin amsa sammacin yan sanda a Kaduna.
Mujjalar ta ruwaito cewa da an damke 'yar wasan a Abuja amma wani babban jami'in yan sanda ya roki abokan aikinsa su daga mata kafa ta amsa sammaci a Kaduna.
KU KARANTA: Kasancewan Trump shugaban kasar Amurka ta'addancin tattalin arzikin ne garemu - Shugaban kasar Iran
A wasikar babban hadimin IGP ya aikewa kwamishanan yan sandan jihar Kaduna, ya bukaceshi yayi abinda ya kamata domin tabbatar da cewa abinda tayi bai haifar da rikici ba.
"Ina mai aika maka umurnin Sifeto Janar na yan sanda cewa ka dauki matakin da ya dace wajen tabbatar da cewa wannan abu bai haifar da wani rikici ko tashin hankali ba."
"Sifeto Janar na yan sanda na baka umurnin cewa ka aiko masa rahoton yadda abin ya kasance," DCP Idowu ya rubuta a wasikan.
KU KARANTA: Kasancewan Trump shugaban kasar Amurka ta'addancin tattalin arzikin ne garemu - Shugaban kasar Iran
Mun kawo muku cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Rahata Sadau, ta bayyana cewa ta zama abin tausayi sakamakon hotunanta da ta saka wadanda suka haddasa cin mutunci ga addininta.
Rahama wacce tun da fari ta fito ta nuna nadama a kan wallafa hotunan da ta yi, bayyana cewa ta ji zafi matuka kan yadda abokan sana’anta suke ta maganganu kan al’amarin.
Ta jaddada cewa abun ya faru ne ba tare da san ranta ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng