Da duminsa: IGP ya janye yan sandan dake kare Fani Kayode, Sanatoci, manyan malamai da masu kudi a fadin tarayya
- A karo na biyu cikin yan makonni, IGP Adamu ya aikewa kwamishanoni da kwamandoji sakon kar a kwana
- Tun bayan rikicin EndSARS, an bukaci a janye yan sandan dake tare da manyan masu kudi da fada a ji
- Yawancin jami'an yan sandan Najeriya na tsare yan siyasa, attajirai, dss maimakon jama'ar kasa
Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin janye dogaran dake wajen attajirin dan kasuwa, Emeka Offor; Fani-Kayode, manyan malamai da kamfanoni da fadin tarayya.
Wannan umurni ya shafi mutane 60, kamfanoni, cocuna da kungiyoyin addini.
Daga ciki akwai Christ Embassy, Think Nigeria First Initiative, Uche Sylva International, Stanel Groups, da KYC Holding
Sauran sune Sen Lado Yakubu, Amb. Yuguda Bashir, Uche Chukwu, Sen. Boroface Ajayi, Mutiu Nicholas, Sen. Tokunbo Afikuyomi, Edozie Madu, David Adesanya, Chris Giwa, Chief Godwin Ekpo, Chief Pius Akinyelure da sauransu.
Hakan na kunshe cikin wasika mai lamba .CB: 4001/IGP.SEC/ABJ/VOL.116/32 da rana wata 4 ga Nuwamba, da IGP ya aikewa dukkan kwamishanonin yan sandan jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya.
KU DUBA: Sabbin mutane 223 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 63,731
KU KARANTA: Kasancewan Trump shugaban kasar Amurka ta'addancin tattalin arzikin ne garemu - Shugaban kasar Iran
Mun kawo muku cewa a ranar 21 ga Oktoba, IGP Adamu ya aika sakon waya ga dukkan kwamishanonin yan sanda cewa su janye dogaran daidaikun mutane inda yayi gargadin cewa duk wanda bai bi umurnin ba zai fuskanci ukuba.
Amma duk da hakan, akan ga manyan masu kudi da yan siyasa da jami'an yan sanda.
Saboda haka a wasikar da PSO na IGP, DCP Idowu Owohunwa, ya rattafa hannu ranar 4 ga Nuwamba, an lissafa sunayen wadanda za'a janye dogaransu.
Bayan haka, IGP ya umurci manyan yan sandan su turo masa rahoton da ke nuna sun bi umurninsa nan da ranar 10 ga Nuwamba.
A bangare guda, sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin gudanar da bincike kan 'yar wasar dirama, Rahama Sadau, kan cece-kucen da ya biyo bayan hotunan tsiraicin da ta wallafa kan dandalin sada zumunta.
'Yar wasan diraman ta daura wasu hotuna kuma hakan ya haddasa kalaman batanci ga manzon Allah (SAW).
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng