Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya sun taya Biden murna

Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya sun taya Biden murna

- Shugaba Muhammadu Buhari da takwarorinsa na kasashen duniya sun taya Joe Biden murnar lashe zabe

- Bayan taya murnar, Buhari ya yi fatar Mista Biden zai kyautata alaka da Najeriya da Afirka musamman a bangarori kamar tattalin arziki, tsaro, siyasa da diflomasiyya

- Sauran kashashen da suka taya Biden murna sun hada ba Burtaniya, Greece, Ireland, Canada, Jamus, Faransa, Beligium da sauransu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban Amurka Joe Biden murna kan zabensa a matsayin sabon shugaban Amurka.

Buhari a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a daren ranar Asabar ya yi kira ga Mista Biden ya "ya kara kusantar kasashen Afirka bisa girmama juna da batutuwan da juna za su amfana."

Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya sun taya Biden murna
Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya sun taya Biden murna. Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Da ya ke magana kan alakar kasa da kasa, ya bukaci zababben shugaban kasar "ya yi amfani da kwarewarsa wurin magance mummunan siyasar son kai na kawai a siyasar duniya da ya janyo rarrabuwar kawuna."

DUBA WANNAN: Trump ya yi watsi da nasarar Biden, ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su zabi shugaban kasa ba

"Nasarar ka darasi ne da ke tunatar da mu cewa demokradiyya ce tsarin gwamnati mafi kyau don tana bawa mutane damar canja gwamnati cikin lumana," in ji Buhari.

Har wa yau, Buhari ya ce yana fatan samun ganin hadin kai tsakanin Najeriya da Amurka musamman bangarorin tattalin arziki, diflomasiyya, siyasa da tsaro.

KU KARANTA: Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka

Sauran shugabanni kasashen duniya suma sun bi sahun Buhari wurin mika sakon taya murna ga Mista Biden.

Cikin wadanda suka mika sakon taya murnar akwai shugabannin kasashen Ireland, Canada, Burtaniyya, Faransa da Jamus.

Sauran su ne Greece, Belgium da Tarayyar kasashen Turai.

A wani labarai, kungiyar malam jami'a (ASUU) a ranar Juma'a ta roki gwamnatin tarayya ta taji tausayin yayan talakawan Najeriya, ta kuma gaggauta amincewa da bukatar domin kuwa sun gaji da yajin aiki.

Kungiyar tace gwamnati na matsa mata akan ta janye yajin aikin ne, saboda ganin irin barnar da matasa suka yi lokacin zanga zangar Endsars kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel