Mun gaji da yajin aiki, ku tausayawa yaran talakawa, ASUU ta roki FG
- Da gayya gwamnati taki biyan bukatun mu saboda yaran su ba a Najeriya suke karatu ba
- Ba shiga tsarrin IPPIS ne ya janyo yajin aiki ba, alkawuran da aka kasa cika mana ne
- Zanga-zangar EndSARS ta ta'azzara ne don yadda matasa suka gaji da zaman gida bayan shafe kusan shekara guda
Kungiyar malam jami'a (ASUU) a ranar Juma'a ta roki gwamnatin tarayya ta taji tausayin yayan talakawan Najeriya, ta kuma gaggauta amincewa da bukatar domin kuwa sun gaji da yajin aiki.
Kungiyar tace gwamnati na matsa mata akan ta janye yajin aikin ne, saboda ganin irin barnar da matasa suka yi lokacin zanga zangar Endsars kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Kungiyar ASUU shiyyar Akure wanda ta hada da shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta Akure, Dr. Olayinka Awopetu, Jami'ar jihar Ekiti, Dr. Kayode Arogundade, da sauran shugabannim shiyyar ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai.
DUBA WANNAN: An sake zaɓen sabbin 'yan majalisu musulmai a Amurka
Sanarwar wadda mai kula da shiyyar, Prof. Olu Olufayo ya fitar tayi bayani cewa dalilin da yasa suke ci gaba da yajin aiki shine gwamnati ta gaza cika musu alkawarin data daukar musu tsakanin 2013 zuwa 2019 bawai saboda tsarin biyan albashi na IPPIS ba.
Ya ce: "Saboda kawar da kokwanto, muna fafutuka ne akan; farfado da jami'o'in gwamnati, biyan kudaden alawus, duba jami'o'in don cika alkawarin da gwamnatin tarayya. Tun shekarar 2009, muke zuwarwa gwamnati da batun akan ayi adalci a cika mana alkawari, wannan shine dalilin yajin aikin."
KU KARANTA: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona
A cewarsa, "Mun gaji da yajin aikin nan. Yayanmu makarantun gwamnatin suke yi, kuma abin haushi gwamnati ta kasa biyan bukatun mu, yayan su ba a Najeriya suke karatu ba. Abin takaici. Da gayya gwamnati take matsawa mu dawo kafin su cika alkawarin da sukayi."
"Yaran mu suna zaune a gida kusan shekara, ba laifin mu bane, mun fara yajin aiki tun kafin zuwan annobar Corona kuma dalibai sun gaji, yana cikin abin da ya ta'azzara zanga zangar Endsars kuma gwamnati tasan haka. Suna maganar sulhun da muka dade muna nema watanni da suka gabata. Nasan daliban jami'ar jihar Kwara sun bawa gwamnati sati biyu ko a koma makaranta ko su cika tituna da zanga zanga. Abin da yasa gwamnati take matsawa sai mun koma."
Ya kuma shawarci gwamnati da ta tausayawa iyayen da basu da halin tura yaransa waje domin yin karatu. Kuma ya ce " kada al'umma su zargi ASUU da yunkurin lalata makarantu, saboda laifin gwamnatin tarayya ne."
A wani labarin, kun ji cewa Jami'an Hukumar Kiyayye Hadurra na Kasa, FRSC, za su fara amfani da bindiga don kare kansu daga sharrin wasu masu amfani da tituna a Najeriya.
Akinfolarin Mayowa, shugaban kwamitin FRSC a majalisar wakilai ta kasa ne ya sanar da hakan yayin kare kasafin kudin hukumar na 2021 a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba a Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng