Harbin Lekki: Ministocin kudu maso yamma sun bukaci a binciki sojoji

Harbin Lekki: Ministocin kudu maso yamma sun bukaci a binciki sojoji

- Ministocin kudu maso yamma wadanda suka koma jihohinsu sun mika rahoto ga FEC a ranar Laraba

- Rahoton da suka mika ya kunshi bukatar yin bincike sosai a kan al'amarin da ya faru a Lekki Toll gate

- Ministocin sun bukaci hakan ne don tabbatar da gaskiyar lamarin da ya faru

Ministocin kudu maso yamma da aka umarta da su koma jihohinsu na gado saboda rikicin zanga-zangar EndSARS sun gabatar da rahoto ga majalisar zartarwa ta tarayya.

A rahoton da suka gabatar a ranar Laraba da safe, sun bukaci a yi bincike mai tsanani a kan harbin da sojoji suka yi a Lekki Toll Gate, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, wasu mutane masu kayan sojoji sun iso Lekki Toll Gate ana tsaka da zanga-zanga, inda suka fara harbe-harbe, wanda hakan yayi sanadiyyar watsa masu zanga-zangar da dama, wasu kuma suka tsere, garin haka suka ji munanan raunuka.

Al'amarin ya janyo hankalin mutanen ciki da wajen kasar nan, inda wasu ke ganin an kashe mutane da dama wasu kuma na karyatawa.

KU KARANTA: Hotuna: Shekau ya saki sabon bidiyo tare da kananan yara da ya horar, ya aike sako

Harbin Lekki: Ministocin kudu maso yamma sun bukaci a binciki sojoji
Harbin Lekki: Ministocin kudu maso yamma sun bukaci a binciki sojoji. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Malami: 'Yan daba sanye da kayan sojoji ne suka yi harbe-harbe a Lekki

A wani labari na daban, fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya kwarara addu'o'i ga Rahama Sadau a kan batancin da aka yi wa manzon Allah a karkashin hotunan da ta wallafa.

Kamar yadda ake gani, wadannan hotunan sun matukar janyo cece-kuce da maganganu kala-kala daga jama'a daban-daban.

Daga cikin abinda ya sake tada hankulan jama'a shine wani tsokaci da daya daga cikin abokan jarumar ya yi a karkashin hotunan, lamarin da yasa ta fito ta barranta kanta daga tsokacin tare da nuna nadamarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel