Kotu ta umarci jihar Kogi da ta biya korarren mataimakin gwamna N180m

Kotu ta umarci jihar Kogi da ta biya korarren mataimakin gwamna N180m

- Kotun masana'antu ta kasa, da ke zama a Abuja ta umarci gwamnatin jihar Kogi da ta biya tsohon mataimakin gwamnan jihar N180,000,000

- A watan Oktoban 2019 ne 'yan majalisar jihar suka tsige Simon Achuba daga matsayin mataimakin gwamna a bisa zarginsa da rashin da'a

- Bayan tsige shi ne ya maka gwamnatin a kotu, inda ya bukaci ta biya shi kudadensa da ba a ba shi ba lokacin yana mataimakin gwamnan jihar

Kotun masana'antu ta kasa da ke zama a Abuja, ta umarci gwamnatin jihar Kogi, da ta biya tsohon mataimakin gwamnan jihar, Simon Achuba, naira miliyan 180.

Alkalin kotun, mai shari'a Oyebiola Oyewunmi, ya umarci gwamnatin jihar da ta biya kudin cikin kwanaki 30 da ribar kaso 30 bisa dari na kowanne wata.

Kotun ta share wa Achuba hawayensa, inda ta bukaci a biya shi naira miliyan 328.32,000 a matsayin ribar da ta hau kudin.

Achuba ya kai karar gwamnatin jihar Kogi ga kotun masana'antu ta kasa, inda ya bukaci gwamnatin ta biya shi kudadensa da ta rike.

Kotu ta umarci jihar Kogi da ta biya korarren mataimakin gwamna N180m
Kotu ta umarci jihar Kogi da ta biya korarren mataimakin gwamna N180m. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta dage dokar ta-baci a dukkan jihar

Ya bukaci a biya shi N921,572,758 na tsaron lafiyarsa, kudin tafiye-tafiye, da sauran kudaden da yakamata a biya shi lokacin yana mataimakin gwamnan jihar.

'Yan majalisar jihar Kogi sun tsige Achuba a watan Oktoban 2019, Punch ta wallafa.

Bayan sun tsigeshi, sun mika rahoto ga shugaban alkalai, Alkali Nasir Ajana, don yayi bincike a kan zargin rashin da'ar tsohon mataimakin gwamnan.

KU KARANTA: Harbin Lekki: Ministocin kudu maso yamma sun bukaci a binciki sojoji

A wani labari na daban, karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya ce an tura wa wasu malaman jami'an sama da asalin albashinsu, har wasu suka mayar wa da gwamnati kudinta, ChannelsTV ta ruwaito.

Ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ake tattaunawa dashi a gidan talabijin din Channels, inda yace ASUU ta lalata tsarin IPPIS, inda aka biyasu fiye da albashinsu, har wasu suka mayar da ragowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel