CNG ta caccaki gwamnonin arewa, ta ce sun nuna rashin muhimmanci ga tsaro, matasa da talauci

CNG ta caccaki gwamnonin arewa, ta ce sun nuna rashin muhimmanci ga tsaro, matasa da talauci

- CNG ta nuna alhininta a kan yadda taron NGF ya kaya wanda gwamnoni da shugabannin arewa suka yi a Kaduna

- Ta ce maimakon taron ya tattauna a kan manyan matsalolin arewa sai ya karkata a kan matsalar EndSARS da ta kafafen sada zumunta

- Kakakin CNG, Abdulazeez Suleiman, ya sanar da hakan a wani taro da suka yi, inda yace hakan ya ba wa 'yan arewa takaici

A jiya ne CNG ta kushe taron da NGF suka yi a Kaduna, ta ce maimakon taron ya karkata matsalolin arewa kamar harkokin tsaro, rikicikin matasa, rashin ayyukan yi, talauci, harkar noma da tabarbarewar tattalin arziki, sai ya karkata a kan kananun matsaloli.

A wani taro da CNG tayi jiya a Kaduna, ta ce maimakon NGF ta mayar da hankali a kan manyan matsaloli, sai suka karkata a kan rikicin EndSARS da kuma matsalolin kafafen sada zumuntar zamani wanda hakan ba itace babbar matsalar arewa ba a yanzu.

Kakakin CNG, Abdulazeez Suleiman ya bayyana a taron da shugabannin gargajiya, mambobin majalisar dattawa, sifeta janar na 'yan sanda da shugaban ma'aikatan shugaban kasa, inda yace: "Mun yaba yadda shugaban kungigar gwamnonin arewa, Simon Lalong ya jajirce wurin tabbatar da hada wannan taron don tattauna matsalolin da suka taso."

CNG tace bata da matsala da matsalolin da NGF suka taso da su kamar, gaggawar daidaitawar ASUU da FG, matsalolin kafafen sada zumuntar zamani wurin yada labaran bogi da sauransu, Vanguard ta ruwaito.

Ta ce NGF ta fi bayar da hankalinta wurin tattaunawa a kan matsalar EndSARS da matsalolin kafafen sada zumunta, wanda wadannan ba su bane manyan matsalolin da ke addabar arewa ba a yanzu haka.

Kamar yadda Suleiman ya bayyana, "CNG da 'yan arewa da dama sun yi mamakin yadda Gwamnoni, shugabannin gargajiya, wadanda arewa suka zaba a matsayin shugabanni da masu matsayi a gwamnati za su taru musamman amma sai su karkata wurin tattaunawa a kan EndSARS da kafafen sada zumuntar zamani maimakon su tattauna a kan manyan matsalolin arewa kamar rashin tsaro, damuwar matasa, rashin ayyukan yi, talauci, tabarbarewar harkokin noma da sauran matsalolin tattalin arziki."

KU KARANTA: IPPIS: Mun biya malamai fiye da albashinsu, sai da wasu suka maido da ragowa- Minista

CNG ta caccaki gwamnonin arewa, ta ce sun nuna rashin muhimmanci ga tsaro, matasa da talauci
CNG ta caccaki gwamnonin arewa, ta ce sun nuna rashin muhimmanci ga tsaro, matasa da talauci. Hoto daga @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Mafi yawan 'yan sandan Najeriya nagari ne - IGP Adamu

A wani labari na daban, ministocin kudu maso yamma da aka umarta da su koma jihohinsu na gado saboda rikicin zanga-zangar EndSARS sun gabatar da rahoto ga majalisar zartarwa ta tarayya.

A rahoton da suka gabatar a ranar Laraba da safe, sun bukaci a yi bincike mai tsanani a kan harbin da sojoji suka yi a Lekki Toll Gate, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel