Taron ASUU da FG: An tashi dutse a hannun riga, za a cigaba da yajin aiki

Taron ASUU da FG: An tashi dutse a hannun riga, za a cigaba da yajin aiki

- Taron da ASUU tayi da FG a ranar Laraba ba a samu wata nasara ba, har yanzu basu cimma matsaya ba

- FG ta ce za ta iya bawa ASUU naira biliyan 20 maimakon 110 da suka bukata saboda tabarbarewar arzikin kasa sakamakon COVID-19

- ASUU ta ki amincewa da hakan, inda tace dama gwamnatin tarayya bata cika mata alkawari da yarjejeniyarsu ba tun 2007

Taron da ASUU tayi da FG bai haifar da da mai ido ba, inda suka rabu a uwa kuturwa, kaka mayya.

Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya ce gwamnatin tarayya bata da Naira biliyan 110 da ASUU take bukata a hannunta.

Ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba lokacin da suke tsaka da taron, inda yace za su iya ba wa ASUU naira biliyan 20 saboda halin tabarbarewar arziki da Najeriya take ciki.

Idan ba a manta ba, ASUU ta tafi yajin aiki tun watan Maris a kan rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta dauka tun 2009, da kuma yarjejeniyar da tayi da FG wacce ta sa hannu a 2013 da 2017.

ASUU ta ki amincewa da tsarin biyan albashin IPPIS wanda gwamnatin tarayya ta gabatar mata.

A taron, sun tattauna a kan yadda gwamnatin tarayya ta gabatar wa da ASUU naira biliyan 20, maimakon naira biliyan 110 da ta bukata, kuma gwamnati tace babu gudu babu ja da baya, tana nan a kan wannan tsarin.

Sannan gwamnati ta ce saboda tabarbarewar arziki sakamakon annobar COVID-19, ba za ta iya bayar da naira biliyan 110 ba naira biliyan 20 don gyara, naira biliyan 30 kuma na kungiya, duka gaba daya naira biliyan 50.

A cewar Ngige, ASUU tace za ta amince da naira biliyan 30 don ta rabawa malamai, banda sauran kungiyoyi 3 da ke karkashin ta. Kuma gwamnati ba za ta iya bayar da wani kudin na daban ba.

Ngige ya kara da cewa, gwamnati za ta yi wani taro a ranar Juma'a, za ta tuntubesu idan akwai bukatar su kara yin wani taron na daban.

KU KARANTA: Hotuna: Shekau ya saki sabon bidiyo tare da kananan yara da ya horar, ya aike sako

Taron ASUU da FG: An tashi dutse a hannun riga, za a cigaba da yajin aiki
Taron ASUU da FG: An tashi dutse a hannun riga, za a cigaba da yajin aiki. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbin Lekki: Ministocin kudu maso yamma sun bukaci a binciki sojoji

A wani labari na daban, Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce akwai yuwuwar 'yan daba ne suka saka kayan sojoji sannan suka dnga harbe-harbe a Lekki tollgate da ke jihar Legas.

Kusan makonni biyu da suka gabata ne matasa suka fara zanga-zanga inda suka bukaci a kawo karshen zaluncin 'yan sanda a fadin kasar nan.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi bukatar inda ya rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng