Kasancewan Trump shugaban kasar Amurka ta'addancin tattalin arzikin ne garemu - Shugaban kasar Iran
Shugaba kasar Iran, Hassan Rouhani, a ranar Asabar ya ce yana kyautata zaton cewa yanzu yakamata duk wanda zai zama sabon shugaban kasan Amurka ya san cewa takunkumi ba zai tursasa Iran sallamawa Amurka ba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, wanda ke hanyar sauka daga kujerarsa ya tsananta takunkumi kan Iran tun 2018 da ya janye daga yarjejeniyar karfin nukiliyan da Obama yayi da Iran.
"Muna kyautata zaton cewa abubuwan da suka faru shekaru uku da suka gabata zai zama darasi ga sabon gwamnatin Amurka kan komawa kan yarjejeniyar da akayi da ita," Rouhani ya bayyana a jawabi, Punch ta dauko.
"Al'ummarmu sun fuskanci ta'addancin tattalin arziki shekaru ukun da suka gabata kuma mun nuna jajircewa da hakuri."
Rouhani yace Iran zata "cigaba da jajircewa da hakuri har sai Amurka ta bi doka."
Shugaba kasan ya ce "wadanda suka kakaba mana takunkumi sun gano cewa kuskure ne kuma ba zasu cimma manufarsu ba ta wannan hanyar."
Iran tace idan har Amurka na son komawa kan yarjejeniyar nukiliyan da Trump ya janye, wajibi ne ta hada da diyya bisa asaran da Iran tayi kuma tay alkawarin ba zata sake haka ba.
Asali: Legit.ng