Sanata Ladoja ya mayarwa Obasanjo martani kan batun tsige shi a matsayin gwamna a 2006

Sanata Ladoja ya mayarwa Obasanjo martani kan batun tsige shi a matsayin gwamna a 2006

- Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo martani kan jawabin da ya yi game da tsige shi a 2005

- Obasanjo a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba ya yi ikirarin cewa an tsige Ladoja ne don ya ki yi wa marigayi Lamidi Adedibu ɗa'a

- Sai dai Ladoja ya bayyana kalaman na Obasanjo a matsayin tsantsagwaron karya mara tushe

Tsohon gwamnan Jihar Oyo, Sen. Rashidi Ladoja ya bayyana a jiya cewa labarin da tsohon shugaban kasa Obasanjo kan dalilin tsige shi a shekarar 2005 ba gaskiya bane, inda ya kara da cewa Obasanjo bazai iya wanke kansa daga tsigewar da aka masa ba.

Ya shawarci tsohon shugaba Obasanjo da kada ya dawo da abu baya saboda ba wani da zai yi ya zare hannunsa daga tsigewar da akayi masa a 2005.

Ladoja ya mayar wa Obasanjo martani
Ladoja ya mayar wa Obasanjo martani. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Ali Kwara

Obasanjo ya yi jawabi a wajen taron kaddamar da littafin tsohon Gwamna Adebayo Alao-Akala a Ibadan, inda ya bayyana cewa yadda Ladoja ya kasa yi wa marigayi Lamidi Adedibu da Cif Yekini Adeojo ɗa'a hakan yasa aka tsige shi.

An dai tsige Ladoja daga gwamnan Oyo a shekarar 2005, inda mataimakin sa, Aloa-Akala, ya ci gaba da riqe kujerar, har zuwa lokacin da kotu ta dawo masa da mukamin sa bayan wata sha ɗaya ba tare da mulkin ba.

KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

Da yake maida martani ta hannun mai yada labaransa, Alhaji Lanre Latinwo, Ladoja ya ce maganar Obasanjo "tsantar ƙarya ne kurum"

"Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya manta cewa babbar kotun kasa ta yanke hukuncin cewa tsigewar da aka yi wa Ladoja haramtacciya ce."

Bari mu fadawa Obasanjo gaskiya, shure shuren kaza baya hana mutuwarta, duk wani batancin da zai yi bazai taimake shi ba.

Ya kuma ce tsufa ce ta fara saka Obasanjo manta wasu abubuwan.

"Saboda haka, Ladoja baida wata nadama, yazo ya yi mulki ne gwargwadon iyawarsa, kuma sakamakon hakan ya samu ƙaunar da mutanensa keyi masa har zuwa yanzu," Latinwo ya faɗi a jawabinsa

A wani labarin daban, mutanen garin Kungurki a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara sun daƙile harin da ƴan bindiga suka kai musu a cewar rahoton Daily Trust.

Wasu ƴan garin sun ce ƴan bindigan sun kai musu hari ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin wani mai shago da ɗan bindiga a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel