Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Ali Kwara

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Ali Kwara

- Jarumin mafarauci, shugaban 'yan banga kuma mai yaki da masu laifi, Ali Kwara Azare ya rasu

- Kwara ya rasu ne a Abuja bayan fama da jinya kamar yadda majiya daga iyalansa suka sanar

- Shugaba Buhari ya mika ta'aziya ga gwamnati da al'ummar Bauchi inda ya yi addu'ar Allah saka wa Ali Kwara da Aljannah

Shugaba Muhammadu Buhari a daren ranar Juma'a ya ce ba za manta da gudunmuwar da jarumin mafarucin, shugaban 'yan banga kuma mai yaki da masu laifi ya bada ba wurin 'dakile masu laifi da masu tada kayar baya a cikin daji ba.'

Shugaba Buhari, cikin sakon da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ya yi alhinin rasuwar jarumin da ya bada gudunmawa wurin yaki da masu laifi.

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Ali Kwara
Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Ali Kwara. Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: An yi wa 'yar gidan sarautar Saudiyya fashi

"Jarumtar da mafaraucin ya yi wurin taka wa 'yan bindiga, 'yan fashi da'yan ta'adda birki a kusan dukkan jihohin arewa 19 ba boyeyyen abu bane, gwamnati ta kawo shi Abuja ne don cigaba da kula da jinyarsa," a cewar sanarwar.

Ya ce fadar shugaban kasa a daren ranar Alhamis ta bada jirgin sama da zai kai gawar mammacin zuwa filin tashin jirage na Dutse inda daga nan za a tafi da shi garinsa na Azare a Jihar Bauchi inda za a yi masa jana'iza.

KU KARANTA: Mutanen gari sun fatattaki 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara

"A madadin gwamnati da dukkan mutanen kasa, ina mika ta'aziyya ga gwamnatin Bauchi da al'ummar jihar bisa rasa wannan jarumin da ya sadaukar da rayuwarsa don taimakawa jami'an tsaro yaki da bata gari."

"Ba za a manta da rawar da Ali Kwara ya taka ba wurin dakile shu'uman masu laifi a dazuka. Muna godiya da kokarinsa, da yawa cikin masu laifin sun tuba inda wasu da dama suka fuskanci hukunci. Samun jarumai irinsa abu ne mai wuya a wannan zamanin. Allah ya saka masa da gidan Aljannah," a cewar sanarwar.

A wani labarin, kungiyar malam jami'a (ASUU) a ranar Juma'a ta roki gwamnatin tarayya ta taji tausayin yayan talakawan Najeriya, ta kuma gaggauta amincewa da bukatar domin kuwa sun gaji da yajin aiki.

Kungiyar tace gwamnati na matsa mata akan ta janye yajin aikin ne, saboda ganin irin barnar da matasa suka yi lokacin zanga zangar Endsars kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164