Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a gadar Kara a Legas

Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a gadar Kara a Legas

- Wata babban mota na dakon man fetur ta yi gobara a babban titin Legas zuwa Ibadan

- Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe ɗaya na daren ranar Asabar 7 ga watan Nuwamban 2020

- Jami'an hukumar bada agajin gaggawa na Legas, LASEMA, sun isa wurin don kashe gobarar

Wata tanka maƙare da man fetur da kama da wuta ta gadan Kara da ke babban titin Legas zuwa Ibadan.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa misalin ƙarfe ɗayan daren ranar Asabar 7 ga watan Nuwamba ƴan kwana-kwana ba su isa wurin ba.

Yanzu-yanzu: Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a gadar Kara
Yanzu-yanzu: Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a gadar Kara. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben Amurka: Joe Biden ya ce zai mayar da Amurka cikin yarjejeniyar Paris Accord

Cinkoson ababen hawa ya ritsa da matafiya da dama da ke fitowa daga Legas don zuwa wasu garuruwan.

Wakilin majiyar Legit.ng Hausa da ya samu ikon ganin abinda ke faruwa a wurin ya ce akwai wasu motocci da gobarar ta ritsa da su.

Kalli bidiyon yadda motocci suka kone sakamakon gobarar tankar:

KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

Wasu masu motocci kuma sun fara juyawa suna aron hannu don gudun cinkoson ababen hawa ya ritsa da su a gadar da motoccin ke ci da wuta.

A wani labarin, wani mutum ya rubutawa wata coci bukatar a dawo masa da duk abin da ya bayar a matsayin baiko da sadaka ga cocin tsawon shekara 19.

Dishon Kinyanjui Kinuthia, wani kirista dan Kenya, ya rubata wasikar ta shafin Tuwita ga Cocin kuma ya yi gargadin cewa zai dauki mataki idan ba'a dawo masa da kudadensa ba.

Dishon, wanda ya ke halartar Cocin Revival Mission Church, Kabete, a Nairobi, ya ce ya kasance yana halartar cocin daga shekarar 1997 kafin ya bar cocin a 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel