Zaben Amurka: Joe Biden ya ce zai mayar da Amurka cikin yarjejeniyar Paris Accord

Zaben Amurka: Joe Biden ya ce zai mayar da Amurka cikin yarjejeniyar Paris Accord

- Ɗan takarar jam'iyyar Democrats a zaɓen shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya wani muhimmin aiki da zai yi idan ya zama shugaban ƙasa

- Joe Biden ya ce cikin kwanaki 77 zai mayar da Amurka cikin ƙasashen da ke yarjejeniyar Paris Accord

- Shugaban Amurka Donald Trump ne ya janye Amurka daga yarjejeniyar tun a Yunin shekarar 2017

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Democrat, Joe Biden ya sha alwashin warware matakin da Shugaba Donald Trump na ficewa daga Paris Accord.

Amurka ce ƙasa ta farko da ta fara ficewa daga yarjejeniyar ta ƙasa da ƙasa na sauyin yanayi.

Trump ya sanar da ficewar Amurka a Yunin 2017 amma sai ranar 4 ga watan Nuwamba ficewar zata fara aiki kamar yadda dokokin Majlisar Ɗinkin Duniya ta tanada.

Zaben Amurka: Joe Biden ya bayyana abu na farko da zai fara warwarewa cikin kwanaki 77 na shugabancinsa
Dan takarar shugaban kasa na Democrat. @JoeBiden
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

A halin yanzu da sakamakon zaben shugaban Amurka ke nuna alamun Biden ne zai yi nasara, ya ayyana cewa zai bawa canjin yanayi muhimmanci.

"A yau, gwamnatin Trump za ta fice daga yarjejeniyar canjin yanayi na Paris a hukumance. Cikin kwanaki 77, gwamnatin Biden za ta sake shiga yarjejeniyar," Inji Biden da ake fatar zai yi rantsuwar kama aiki a ranar 20 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu hayar shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu

Biden ya gabatar da shirinsa na amfani da Naira Tiriliyan 1.7 don rage adadin iskar carbon da Amurka ke fitarwa zuwa shekarar 2050.

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel