EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici

EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici

- Sifeta janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu ya ce kafafen sada zumunta ne suka assasa rikicin SARS

- A cewarsa, bata-gari sun yi zanga-zangar ne musamman don su yi sata kuma su hargitsa kasa

- Ya fadi hakan ne a lokacin da ya kai wa gwamna Uzodimma na jihar Imo ziyara don yi masa jaje

Sifeta janar, na 'yan sanda, Muhammad Adamu, ya ce kafafen sada zumuntar zamani su ne makaman da suka assasa rikicin EndSARS a jihohin Najeriya.

IGP din ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ga gwamna Hope Uzodimma don yi masa jaje a kan asarar da masu zanga-zangar EndSARS suka tafka a jiharsa.

"Na zo ne musamman don duba asarorin da aka tafka a wuraren 'yan sanda a jihar Imo," cewarsa.

Ya ce an yi zanga-zangar ne musamman don 'yan ta'adda su yi sata, su kuma rikita kasar gaba daya, ba don 'yan sanda ko SARS ba.

Ya shawarci 'yan Najeriya da su yi kokarin kiyaye dukiyoyin kasa daga asarori, The Nation ta ruwaito.

Ya umarci 'yan sanda da su jajirce wurin rike ayyukansu yadda ya dace a lokacin zanga-zangar nan.

KU KARANTA: Rashin 'yan sanda: 'Yan fashi sun samu masauki a kan babban titin Benin zuwa Auchi

EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici
EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Na kan yi dariya idan na ji ana cewa ba a son mace mai kiba - Dirarriyar budurwa

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban ma'aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci manyan ma'aikatan gwamnati zuwa wurare daban-daban a cikin kasa a matsayin daya daga cikin ayyukan da matasa suka bukaci a yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da shugabannin gargajiya a kan matsalolin da Najeriya take fama da su, daga Daily Nigerian.

Ya rokesu da su taimaki mulkinsa wurin kwantar da tarzoma musamman wacce matasa suka tayar, a sanar da matasa cewa ya ji kukansu kuma yanzu haka yana iyakar kokarinsa wurin ganin ya daidaita al'amura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel