Da duminsa: Mutum 6 sun harbu da cutar korona a makarantar sakandare

Da duminsa: Mutum 6 sun harbu da cutar korona a makarantar sakandare

- Annobar COVID-19 tana cigaba da yaduwa a jihohi kamar Legas, musamman bayan bude makarantu

- An samu wasu malamai 5 da dalibi daya da ke dauke da cutar a wata makarantar sakandare

- Bayan wata malama ta fadi ciwo a makarantar da ke jihar Legas aka gano sauran masu cutar

Wasu malamai 5 da dalibi daya, sun kamu da cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare da ke jihar Legas.

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da hakan a ranar juma'a, jaridar The Punch ta wallafa.

Kamar yadda takardar mai taken jihar Legas ta tabbatar da samun wasu masu cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare kuma kwamishinan lafiya, Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da hakan.

Wani bangare daga cikin takardar yazo, "Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da kamuwar wasu da cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare ta kwana da ke mainland.

"An samu wata malamar makarantar mai dauke da cutar COVID-19 a ranar 2 ga watan Nuwamba.

"Bayan an bi diddiki, an gano wani dalibi da wasu malamai 4 da ke dauke da cutar.

"Bayan daya daga cikin malaman ya fadi ciwo na wasu 'yan kwanaki, an kai shi asibitin makarantar, inda aka fara kula da lafiyarsa. Da aka yi wa malaman gwajin COVID-19 sai aka gano suna dauke da cutar a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba."

KU KARANTA: INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin

Da duminsa: Mutum 6 sun harbu da cutar korona a makarantar sakandare
Da duminsa: Mutum 6 sun harbu da cutar korona a makarantar sakandare. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan sarakuna da shugabanni na jihar da su mayar da hankalinsu wurin zama a masarautunsu tare da kiyaye zuwa waje suna kwana.

Ya sha alwashin yin maganin dukkan masu bada gudumawa a yankin wurin ta'azzarar rashin tsaro. Ya ce dukkan mai sarautar da aka kama zai rasa kujerarsa.

Gwamna Bello Matawalle ya sanar da hakan ne yayin bude taron kwana daya a kan tsaro wanda yayi da sarakunan gargajiya, malamai da kuma shugabannin cibiyoyin tsaro a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel