Jami'an FRSC za su fara amfani da bindiga a tituna - Majalisa

Jami'an FRSC za su fara amfani da bindiga a tituna - Majalisa

- Kwamitin Majalisar Wakilai kan FRSC tana neman a bawa jami'an hukumar ikon rike bindiga

- Kwamitin ta ce dama akwai dokar da ta bawa jami'an hukumar damar rike bindigar so kawai ta ke a aiwatar da shi

- Majalisar ta ce hakan ya zama dole ne don yawaitar barazana ga rayuwan jami'an da masu motocci ke yi

Jami'an Hukumar Kiyayye Hadurra na Kasa, FRSC, za su fara amfani da bindiga don kare kansu daga sharrin wasu masu amfani da tituna a Najeriya.

Akinfolarin Mayowa, shugaban kwamitin FRSC a majalisar wakilai ta kasa ne ya sanar da hakan yayin kare kasafin kudin hukumar na 2021 a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba a Abuja.

Akinfolarin Mayowa ya yi bayanin cewa dokar ta FRSC ACT na 1992 ta bawa jami'an hukumar ikon rike bindiga kamar yadda LIB ta ruwaito.

Jami'an hukumar kiyayye haɗura za su fara rike bindiga - Majalisa
Jami'an hukumar kiyayye haɗura za su fara rike bindiga - Majalisa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wilbur: Hotunan karen da ya lashe zaɓen kujerar magajin gari a Amurka

Ya ce ya zama dole a aiwatar da dokar domin tabbatar da masu amfani da titi suna bin dokoki ta kuma inganta aikin jami'an na FRSC.

A cewarsa, kare haddura a tituna nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan 'yan Najeriya kuma don haka ya kamata a dauki duk matakan da suka dace don cimma wannan.

Ya kara da cewa kwamitinsa za ta gana da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha kuma za ta rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasika game da aiwatar da dokar.

Mamban kwamitin, Solomon Maren ya kara da cewa kwamitin za ta tattauna batun da Sifeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu.

KU KARANTA: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

Dan majalisar ya ce barazana ya karu a tituna don haka ya kamata FRSC su rika amfani da bindiga.

Shugaban FRSC na kasa, Boboye Oyeyemi ya koka kan yadda masu ababen hawa ke yi wa jami'an hukumar barazana.

Oyeyemi ya ce bawa jami'an ikon rike bindiga zai magance direbobi masu niyyar kai wa jami'ansa hari ya kuma kare jami'an.

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel