Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram

Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ce amfani da dabarun soji wurin yakar Boko Haram ba mafita bace

- Ya bukaci gwamnati da ta yi amfani da salon siyasa wurin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin

- Gwamnan ya jaddada cewa matsalar fatara da talauci na taka rawar gani wurin tunzura matasa shiga ta'addanci

Gwamnan jihar Borno, Farfesa babagana Zulum, a ranar Juma'a ya ce shawo kan matsalar tsaro ta hanyar amfani da dakarun soji a kasar nan ba hanya ce mai bullewa ba ga matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso gabas.

Ya ce amfani da salon siyasa wurin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar shine hanya da ta dace, Vanguard ta ruwaito.

Farfesa Zulum ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labaran gidan gwwamnati bayan taron sirrin da yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce yanayin salon da ake amfani da shi a halin yanzu ba zai isa ya kawo karashe matsalar tsaro ba.

Gwamnan ya kara da cewa fatara da tsananin talauci ya taka rawar gani wurin assasa matasalar tsaro. Ya ce dole ne a inganta rayuwar matasa domin gujewa hakan.

Ya yi kira ga gwamnati a kowanne mataki da ta samar da ayyukan yi ga matasa tare da samar da muhalli ga jama'ar da suka bar gidajensu na gado domin samun mafaka.

Ya ce mulkinsa ya dage inda ya mayar da a kalla mutum 100,000 da suka samu mafaka bayan mayakan ta'addancin Boko Haram sun fatattakesu.

Gwamnan ya ce komawar jama'a gidajensu na gado alamu ne da ke nuna cewa tabbas zaman lafiya ya dawo yankin Borno.

KU KARANTA: INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin

Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram
Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan sarakuna da shugabanni na jihar da su mayar da hankalinsu wurin zama a masarautunsu tare da kiyaye zuwa waje suna kwana.

Ya sha alwashin yin maganin dukkan masu bada gudumawa a yankin wurin ta'azzarar rashin tsaro. Ya ce dukkan mai sarautar da aka kama zai rasa kujerarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: