Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo

Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo, ya bayyana dalilinsa na mara wa Shehu Yar'Adua baya, maimakon Olu Falae a 1992

- Ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin kaddamar da Littafin tarihin tsohon gwamnan jihar Oyo, wanda Adebayo Alao-Akala ya rubuta

- Ya ce a lokacin ya duba nagartar Shehu da burinsa na ciyar da Najeriya gaba, maimakon mara wa Olu Falae baya, duk da bayerabe ne dan'uwansa

A ranar Laraba, tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo, ya bayyana dalilin da yasa ya goyi bayan takarar Alhaji Shehu Musa Yar'Adua a kan na Chief Olu Falae a shekarar 1992, yayin shirin zaben shugaban kasa na 1993.

Obasanjo, ya tunatar da hakan ne a lokacin kaddamar da tarihin rayuwar tsohon gwamnan jihar Oyo, littafin Otunba Adebayo Alao-Akala, mai taken: "Amazing Grace," a cewarsa duka 'yan siyasan mataimakansa ne na kusa, a lokacin yana shugaban kasa na mulkin soji.

Ya kara da cewa yardar da yayi da shirye-shiryen Yar'Adua na bunkasa Najeriya shiyasa ya gwammaceshi.

KU KARANTA: Katsina: Gwamnati ta rufe dukkan sansanin 'yan gudun hijira, ta mayar da mutum 27,000 gida

Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo
Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: 2023: Jihohin tsakiya ba za su bi ra'ayin arewa ba - Bitrus ya tabbatar

A cewarsa: "A 1992, Shehu Musa Yar'adua ya zo min da bukatar in yi wa Chief Adedibu magana a maimakonsa. Wannan abu ne da ya san zanyi."

"Sai naje na samu Chief, nayi masa magana, daga ni sai shi, ya amshe ni hannu bibbiyu. Nace masa na san Olu Falae da Shehu Yar'Adua sosai, don sun yi aiki a karkashi na.

"Kuma duk mutanen kirki ne. Amma idan za a duba cigaban kasa, zan ce Shehu yafi Olu, idan kuma za mu kalli cigaba ga Yarabawa, Olu ya fi Shehu."

"Idan kun fahimci zance na, ba yare ne abu na farko da ake kallo ba, cigaban kasa ake kallo. A kan maganar da nayi wa Chief, ya koma bayan Shehu, maimakon Olu a 1992," kamar yadda Obasanjo ya bayyana.

A wani labari na daban, rashin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro yasa mutane sun shiga tsaka mai wuya a titunan Najeriya, inda 'yan ta'adda suka samu dama suna cin karensu babu babbaka.

Jaridar Daily Trust ta wallafa yadda 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane suka fara yadda suka ga dama a titunan Najeriya, tunda suka gano cewa jami'an tsaro basa aiki, musamman 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng