Katsina: Gwamnati ta rufe dukkan sansanin 'yan gudun hijira, ta mayar da mutum 27,000 gida
- Gwamnan jihar Katsina ya umarci 'yan sansanin gudun hijara su koma kauyukansu
- Ya bayar da umarnin nan ne ganin kwanciyar hankali da tsaro ya fara tabbata a jihar
- Gwamnan ya ce duk da haka a shirye ya ke da ya cigaba da taimakon 'yan kauyen da kayan abinci
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe sansanin 'yan gudun hijira a ranar Laraba a jihar, kuma ta umarci mutane 27,000 su koma kauyukansu.
Kwamishinan matasa da habaka wasanni na jihar, Alhaji Sani Danlami, ya bayyana hakan ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar, inda yace za a rufe sansanin gudun hijirar da ke Dandume, Faskari, Kankara, Batsari, Jibia, ATC Katsina da gidan marasa gata da ke Katsina.
Ya ce an yanke shawarar rufe sansanin ne saboda zaman lafiya da samun tsaro da ya fara tabbata a jihar, The Nation ta wallafa.
Yace; "Gwamnatin jihar ta taimaki 'yan kauyakun, inda tace ya kamata su koma gidajensu su don cigaba da rayuwarsu.
"Yau ba a samu kowa ba a sansanin gudun hijira. Duk da har yanzu muna da labarin wasu da ke yawo a cikin gari da sunan 'yan gudun hijira ne."
Danlami ya ce a shirye gwamnatin jihar Katsina take da ta cigaba da taimakon marasa karfi da kayan abinci kafin rayuwarsu ta warware.
KU KARANTA: Majalisa tana tuhumar Lai Mohammed a kan N19m na tafiya da ya karba yayin kulle
KU KARANTA: Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
A wani labari na daban, Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce ma'aikatan gidan gyaran hali suna ta korar wadanda 'yan sanda ke kawo musu a matsayin wadanda ake zargin fursinoni ne suka gudu, saboda rashin kiyaye dokar COVID-19 kamar yadda gidajen gyaran halin suka bukata.
Ministan ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya gama gabatar da kasafin ma'aikatarsa ta 2021 a gaban kwamitin majalisar dattawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng