Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m

Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m

- Wani matashi dan asalin jihar Zamfara amma mazaunin jihar Ogun ya tara miliyan 1 da ribar noma

- Nasir Usman manomin shinkafa da rogo ne a jihar Ogun, inda yace noma tushen arziki ne, don ya gwada kuma ya gani

- Ya shawarci matasa da su rungumi noma, domin ya gwammaci ya narka kudi a gonarsa maimakon kashe wa 'yan mata

Nasiru Usman, wani manomi mai shekaru 29 da haihuwa ya ce ya samu ribar naira miliyan 1 a cikin shekara daya a matsayin ribar noma.

Manomin dan asalin jihar Zamfara, wanda ya ke zama a jihar Ogun ya bayyana hakan a wata tattaunawa da Legit TV suka yi da shi, inda yace yana da burin zama babban manomi a Najeriya.

A cewar manomin shinkafa da rogo a jihar Ogun, ya ce yana da burin kara girman gonar da yake nomawa.

Nasiru ya samu damar tara naira miliyan daya da ribar noma.

Usman ya yi kira ga matasan Najeriya da su rungumi noma don kawar da matsalar rashin aikin yi da talauci.

Ya ce baya son kashe wa mata kudi, ya fi son amfani da kudinsa don yin noma.

KU KARANTA: Dalilin da yasa gidajen gyaran hali basu karbar sabbin masu laifi - Ministan cikin gida

Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m
Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m
Asali: Original

KU KARANTA: Majalisa tana tuhumar Lai Mohammed a kan N19m na tafiya da ya karba yayin kulle

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano wacce Gwamna Abdullahi Ganduje yake jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da daliban makarantar kwana da ke jihar.

Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru, ya sanar da hakan ga manema labarai a kan nasarorin da ma'aikatar ta samu cikin watanni 12, Channel TV ta wallafa.

Ya ce gwamnatin Ganduje ta fi bayar da muhimmanci ga ilimi, musamman yadda yasa shi ya zama kyauta kuma tilas a kan kowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel