APC za ta fara yi wa mambobinta rijista a fadin kasar nan - Buni

APC za ta fara yi wa mambobinta rijista a fadin kasar nan - Buni

- Jam'iyyar APC ta fara amsar kayan rijista na zama cikakken dan jam'iyya

- Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar, Mai Mala Buni ya sanar da hakan a ranar Alhamis

- Ya ce da zarar an gama kai kayan duk jihohin Najeriya, za su sanar da lokacin fara rijistar

A ranar Alhamis, APC ta fara amsar kayan rijistar masu shiga jam'iyya a fadin Najeriya.

Yayin da shugaban kwamitin rikon kwarya na APC da kwamitin tsara harkokin jam'iyya, Mai Mala Buni, ya amshi kayan, ya ce kwanan nan jam'iyya za ta fara rijistar da zarar an gama amsar kayan.

A cewarsa, "kamar yadda kuka gani yau ne muka fara amsar kayan rijistan, wadanda kwanan nan kowacce jiha za ta amshi nata.

KU KARANTA: Jihohin tsakiya ba za su bi ra'ayin arewa ba - Bitrus ya tabbatar

APC za ta fara yi wa mambobinta rijista a fadin kasar nan - Buni
APC za ta fara yi wa mambobinta rijista a fadin kasar nan - Buni. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

"Muna da mazabu 119,000 a cikin kasar nan. Kamar yadda ku ka gani, wadannan kayan rijista ne kuma muna da takardun da mutum zai cika na bayanai a kansa.

"Yau ne muka fara amsar kayan, bayan mun gama amsa, za mu tsayar da ranar da za mu fara rijistar, sannan za mu kara yi wa tsofaffin 'yan jam'iyyar da ke fadin kasar nan rijista." yace.

KU KARANTA: Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m

A wani labari na daban, rashin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro yasa mutane sun shiga tsaka mai wuya a titunan Najeriya, inda 'yan ta'adda suka samu dama suna cin karensu babu babbaka.

Jaridar Daily Trust ta wallafa yadda 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane suka fara yadda suka ga dama a titunan Najeriya, tunda suka gano cewa jami'an tsaro basa aiki, musamman 'yan sanda.

Daily Trust ta bayyana yadda jami'an tsaro suka saki ayyukansu bayan zanga-zangar EndSARS da ta barke a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng