Za a raba kyautar mita sama da miliyan 1 ta wutar lantarki - Buhari

Za a raba kyautar mita sama da miliyan 1 ta wutar lantarki - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sharewa 'yan Najeriya kukansu

- A cewarsa, zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin 'yan Najeriya sun daina biyan haraji

- Ya ce zai tabbatar kudin wutar lantarkin da suka sha kadai za su biya

Shugaban kasa ya ce kowa ya kwantar da hankalinsa, don yanzu haka yana fafutukar ganin cewa 'yan Najeriya sun biya kudin wutar da suka sha kawai, ba tare da wani haraji na daban ba.

Shugaba Buhari yayi wannan alkawarin ne ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, a ranar Laraba.

KU KARANTA: Katsina: Gwamnati ta rufe dukkan sansanin 'yan gudun hijira, ta mayar da mutum 27,000 gida

A cewarsa, yanzu haka gwamnatin tarayya tana kokarin tattara kudaden da za ta samar da mitoci miliyan daya kafin ta samu damar hada mitoci miliyan 6.5 a Najeriya gaba daya.

Kamar yadda Buhari ya wallafa, "A karkashin tsarin shugaban kasa na samar da wuta mita miliyan 1 ba tare da amsar ko sisi daga hannun al'umma ba, yanzu haka an fara kaddamar da shirin a Kano, Kaduna, Legas da Abuja.

"Tsarin da za a sake kaddamarwa zai shafi akalla mutane miliyan 30, don za a yi amfani da mita 6.5 don 'yan Najeriya su amfana."

Za a raba kyautar mita sama da miliyan 1 ta wutar lantarki - Buhari
Za a raba kyautar mita sama da miliyan 1 ta wutar lantarki - Buhari. Hoto daga @newswire
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano wacce Gwamna Abdullahi Ganduje yake jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da daliban makarantar kwana da ke jihar.

Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru, ya sanar da hakan ga manema labarai a kan nasarorin da ma'aikatar ta samu cikin watanni 12, Channel TV ta wallafa.

Ya ce gwamnatin Ganduje ta fi bayar da muhimmanci ga ilimi, musamman yadda yasa shi ya zama kyauta kuma tilas a kan kowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel