Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu hayar shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu

Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu hayar shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu

- Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Adamu Garba ya yi wa kasar Amurka shagube game da zaben shugaban kasarta na 2020

- Adamu Garba ya ce ba a taba yin zabe gurbattace a tarihin Amurka kamar wannan da ake fafatawa tsakanin Donald Trump da Joe Biden ba

- Adamu ya yi wannan maganar ne a martaninsa kan wani rahoto da ke cewa matacce ya lashe zabe inda ya ce Amurka da karbi hayar shugaban INEC

Makonni bayan shigar da mai kamfanin Twitter, Jack Dorsey kara a kotu, tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba ya ce zaben da ake gudanarwa a Amurka cike ya ke da magudi kamar yadda LIB ya ruwaito.

Ya cigaba da cewa yana bada shawaran cewa Amurka ta dauki hayar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, Yakubu Mahmud don ya taimakawa kasar gudanar da zabe 'sahihiya tare da yin adalci.'

Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu aron shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa Adamu
Adamu Garba. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Alkali ya bada belin Naziru Sarkin Waƙa

Adamu ya yi wannan jawabin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba a lokacin da duniya ke jiran sakamakon zaben shugaban kasa da ake fafatawa tsakanin Joe Biden da Donald Trump.

Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu aron shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa Adamu
Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu aron shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa Adamu. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Ya ce;

"Kasar Amurka, #Zaben2020 magudi ko ina. Wannan shine gurbattacen zabe a tarihin Amurka. Da yiwuwar sai mun basu hayar shugaban INEC din mu, Farfesa Yakubu Mohammed."

KU KARANTA: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel