Shugaban kasar Kosovo ya yi murabus don gurfana a gaban kotu

Shugaban kasar Kosovo ya yi murabus don gurfana a gaban kotu

- Shugaban kasar Kosovo yace ya dauki matakin ne don kare martabar kasarsa

- Akwai zarge zarge guda goma akan shugaban da suka shafi aikata laifukan yaki

-An tuhumi tsofaffin masu fafutukar karbawa Kosovo yanci goma da makamancin laifin

Shugaban Kosova Hashim Thaci, ya yi murabus ranar 5 ga watan Nuwamba, don fuskantar shari'a bisa zargin laifukan da suka shafi yaki a Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka da ke birnin Hague.

Shugaban masu fafutukar neman 'yancin kasar daga hannun Serbia a shekarun 1990, ya bayyana Murabus dinsa a wani taron manema labarai a Pristina, babban birnin Kosovo. Ya ce ya dauki matakin ne "don kare martabar shugabancin Kasar Kosovo."

Shugaban kasar Kosovo domin fuskantar zargin laifukan yaki
Shugaban kasar Kosovo domin fuskantar zargin laifukan yaki. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Alkali ya bada belin Naziru Sarkin Waƙa

Ya bayyana a taron manema labarai a birnin Pristina;

"Zan bada hadin kai matuka da adalci. Na yadda da gaskiya, Maslaha da kuma abin da kasar mu zata zama nan gaba."

Ana tuhumar Thaci a wata kotun Kosovo ta musamman da ke zamanta a Hague, Netherlands, wadda aka kafa ta don hukunta laifukan da suka shafi tsofaffin shugabannin ya tawayen Albania.

Tsohon dan gwagwarmayar wanda ya kasance shugaban kasa tun 2016, ya dade yana bayyana cewa bashi da hannu a yakin da da yawa daga cikin yan Kosovo ke kallo "iya" gwagwarmayar kwatar yanci daga Serbia.

KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

Serbia bata amince da bayyana samun yancin Kosovo a shekarar 2008 ba. Serbia da Kosovo sun ta shiga sulhu da yarjejeniya da tarayyar Turai (EU) a kokarin ganin an daidaita dangantaka da kuma bada damar shiga jerin kasashen tarayyar Turai.

Wasu tsofaffin kwamandojin kungiyar (KLA) a Kosovo da suka yi fafutukar kwato yanci daga Serbia suma an tuhume su da laifukan haddasa yaki a kotun kuma an kaddamar da ofishin shigar da manyan kararraki shekara biyar da suka wuce.

Ba a saki bayanin ainihin zargi Goma da ake wa Thaci, Veseli da sauran su ba.

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164