Da duminsa: Kotu ta yi watsi da karar da Trump ya shigar, ta ce a cigaba da gashi

Da duminsa: Kotu ta yi watsi da karar da Trump ya shigar, ta ce a cigaba da gashi

- Wani Alkalin jihar Georgia ya yi watsu da karar Trump dake kalubalantar kuri'un akwatin sako

- Alkali James Bass ya ki sauraron bukatun Trump na tabbatar da cewa an bi dokokin jiha

Wani Alkalin kotun jihar Georgia ya yi watsi da karar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar Amurka, Donald Trump. ya shigar kan kuri'un da aka kada ta akwatin sako.

Alkalin kotun Chatham County, James Basson, a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, ya yi watsi da karar bayan kimanin awa daya da sauraro, Fox2now.com ta ruwaito.

Kwamitin Trump ta bukaci kotun ta tabbatar da cewa an bi dokokin jiha kan kuri'un da mutane suka kada gabanin ranar zabe ta akwatin sako.

Yanzu haka Trump na biye da Biden a zaben.

KU KARANTA: Ciwon kafa ta tasa mutumin da yayi tattaki don nasarar Buhari gaba

Da duminsa: Kotu ta yi watsi da karar da Trump ya shigar, ta ce a cigaba da gashi
Da duminsa: Kotu ta yi watsi da karar da Trump ya shigar, ta ce a cigaba da gashi Hoto: BBC
Asali: UGC

A cewar Wtspp.com, kwamitin yakin neman zaben Trump ta shigar da kara kan wasu kuri'u 53 da ake zargin an shigo da su bayan ranar zabe.

Kwamitin ta ce kada kotu ta bari a kirga kuri'un.

KU DUBA: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da sarakunan gargajiyan Najeriya

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel