Cire kudi da nayi a asusun bankinka babu izininka hakkina ne - Budurwa ga saurayi
- Fusataccen matashin Najeriya ya wallafa hirarsa da budurwarsa da ta matukar tunzura shi
- Kamar yadda hirar ta nuna, budurwar ta cire dubu sittin daga asusun bankin saurayin babu izini
- Ta kuma tabbatar masa da cewa hakan yana daga cikin hakkinta, don haka ba za ta taba tambayarsa ba
Wani matashi dan Najeriya ya wallafa hirarsa da budurwar a kafafen sada zumuntar zamani. Ya wallafa yadda suka yi da ita bayan ta cire kudi daga asusun bankinsa ba tare da izininsa ba.
Kamar yadda hirar ta nuna, budurwar ta nuna rashin nadamarta a kan abinda tayi, sai dai kuma ta bi hakan da korafin cewa baya kula da ita yadda ya dace.
Matashin da ya kasa boye fushinsa ya ja kunnenta a kan sake taba masa kudin asusun bankinsa ba tare da izininsa ba amma ta ce ba za ta daina ba.
Ta tabbatar masa da cewa wasu mazan na nan a kan layi kuma idan ba ya kulawa da ita, za ta karkata garesu.
Ya kara da ja mata kunne a kan cewa ba zai amince da wannan lamarin ba idan kuwa bata kiyaye ba zai iya tsinke alakar a kan hakan.
Ta tabbatar masa da cewa fitar da kudi daga asusunsa hakkinta ne koda kuwa bata sanar da shi ba, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Minista Sadiya Farouk ta yi martani bayan 'yan Najeriya sun bukaci ta yafe musu
KU KARANTA: Da duminsa: Matasa sun banka wa gidan rediyo wuta a jihar Taraba
A wani labari na daban, ana tsaka da raba kayan tallafi a ranar Litinin wasu bata-gari suka dakatar da lamarin, daganan suka kwashe kayan tas sukayi awon gaba dasu, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda Daily Trust ta bayyana labaran jihohin da suka yi ta satar kayan tallafi, sai gwamnatin jihar ta yanke shawarar raba kayan abincin kananan hukumomin da aka ajiye kayan tallafinsu a Ijebu, wadanda suka hada da karamar hukumar Ode, Sagamu da Ifo.
Masu rabawar da suka taru a Ijebu, sun fara raba kayan abincin kenan sai ga bata-garin, wadanda suka kwashe kayan tallafin suka kara gaba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng