Mattacen ɗan takara da korona ta kashe ya ci zaben majalisa a Amurka

Mattacen ɗan takara da korona ta kashe ya ci zaben majalisa a Amurka

- David Andhal, dan takarar jam'iyyar Republican ya rasu sakamakon cutar coronavirus a karshen watan Oktoban 2020

- Jami'an zabe na North Dakota sun ce lokaci ya kure don haka ba za a iya cire sunan Andahl daga takardar kada kuri'a ba

- An sanar da cewa Andahl ya lashe zaben mazabar North Dakota a daren Talata, 3 ga watan Nuwamba bayan samun fiye da 33% na kuri'un da aka kada a zaben

Wani dan jam'iyyar Republican da cutar korona ta kashe a watan Oktoba ya yi nasarar lashe zaben majalisa duk da cewa ya mutu.

An sanar da cewa marigayi David Andhal ne ya lashe zaben mazabar North Dakota a daren ranar Talata 3 ga watan Nuwamba bayan ya samu fiye da kashi 35 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Zaben Amurka: An jefa wa wani dan takara da korona ta kashe kuri'u
Zaben Amurka: An jefa wa wani dan takara da korona ta kashe kuri'u. (Hoto: Twitter/David Andahl)
Asali: Twitter

Cutar COVID-19 ce ta yi ajalin Andahl. An kwantar da shi a asibiti na makonni kafin daga bisani ya rasu yana da shekaru 55 a duniya.

An zabe shi ne tare da Dave Nehring don wakiltar mazabar da ke zaben wakilai guda biyu.

Mutanen biyu sun samu amincewar 'yan republican da masu zabe inda suka kada daya daga cikin 'yan siyasa masu fada aji a North Dakota, Jeff Delzer.

DUBA WANNAN: 'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron

Sakataren gwamnatin jihar Al Jaeger ya shaidawa New York Times cewa jam'iyyar ta Republican wacce ta tsayar da Andahl za ta zabi wani da zai maye gurbinsa.

Ya ce ba kasafai aka fiye samun irin wannan lamarin ba inda ya ce iya saninsa hakan bai taba faruwa ba a shekaru 27 da ya yi yana siyasa.

"A iya sani na, bamu taba samun abu mai kama da wannan ba a baya."

KU KARANTA: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

A wani labarin daban, fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi - Lafia kan abinda suka kira 'batar mazakutar' mutum shida cikin wata guda a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164