Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

- Asuu ta ce gwamnati tafi damuwa da bangarorin bankuna da wutar lantarki fiye da bangaren ilimi saboda anan suke zuba hannun jari

- Idan hakar mu ta gaza cimma ruwa, iyayen yara za su samu ƙarin kashe kudaden da zai janyo wa wasu barin makaranta

- Duk abin da muke muna yi ne don ceto jami'o'in gwamnati daga durƙushewa bawai don bukatar kan mu bane

Kungiyar malaman Jami'a (ASUU) ta ce kada iyaye su yi tunanin cewa abin da suke nema ya yi yawa da har zai sa su dauki dogon lokaci suna yajin aiki.

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana cewa iyaye su lura cewa idan gwagwarmayarsu ta tashi a banza, "aljihun su zai koka wajen tura yaran su karatu jami'a."

Shugaban ASUU shiyyar Lagos, Prof. Olusiji Sowande ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron tattaunawa da kungiyar tayi a jami'ar Olabisi Onabanjo University (OOU), Ago-Iwoye, a jihar Ogun.

Iyayen dalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU
Iyayen dalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Taron ya samu halartar manya manyan jiga jigan kungiyar shiyyar Lagos.

Ya kuma bayyana cewa kungiyar bazata janye yajin aikin ba matukar gwamnati ta gaza cimma bukatun su.

DUBA WANNAN: An kama ɗan tsohon ministan Najeriya ya tafi yin fashi da makami a Abuja

Sowande ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana kokarin batawa kungiyar suna, da yada karya ga al'umma akan halin da ake ciki maimakon maida hankali wajen ganin an kawo karshen matsalar.

Ya ce kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne don ceto jami'o'in gwamnati daga durƙushewa bawai don bukatun kansu ba.

Ya ce, "Gwamnati bata ganin ilimin yan kasa a matsayin abin da zai ceci al'umma sai a matsayin kasuwanci.

KU KARANTA: 2023: Kungiya ta yi barazanar yin ƙarar El-Rufai a kotu idan ya ki fitowa takarar shugaban kasa

"Gwamnati tafi maida hankali wajen ceto Bankuna, Kamfanonin raba wutar lantarki, da Kamfanonin jiragen sama, inda anan suke zuba hannun jari, batun ace wai babu kudin da za a sake gina makarantun da muke dasu, ba karbabben uzuri bane ga kungiyar mu.

"Iyaye da dalibai kada kuyi tunanin ASUU ta bukaci da yawa don ceto makaruntun mu.

"Ya kamata iyaye su fahimci cewa, idan fafutukar mu ta gaza, Aljihun su ne zai koka wajen tura yaransu makaranta, a hakan ma, idan bai yi sanadiyar fitar da yawa daga makaranta ba."

A wani labarin, Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164