Gidauniyar Dangote ta tallafawa Mata 24,000 a jihar Sakkwato

Gidauniyar Dangote ta tallafawa Mata 24,000 a jihar Sakkwato

A ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban 2019, gidauniyar Dangote ta hamshakin attajirin nan, Aliko Dangote, ta bai wa wasu mata kimanin 23,990 tallafin Naira miliyan 239.9 a jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dangote ya ce wannan tallafi na daya daga cikin shirin nan na gidauniyarsa mai sunan Micro Grant Scheme, na bai wa mabukata tallafi domin inganta jin dadin rayuwar al'umma.

Shirin Micro Grnat Scheme na daya daga cikin shirye-shiryen tsamo al'ummar Najeriya daga talauci tare da bunkasa tattalin arziki wanda gidauniyar Dangote ta assasa da manufar agaza wa kokarin da gwamnatin ke yi a kasar.

An kaddamar da shirin ne tsawon shekaru kalilan da suka gabata, inda gidauniyar Dangote ke bibiyar tafarkin wani tsari da ta shimfida wajen tallafa wa mata kimanin dubu daya a kowace karamar hukumar da ke fadin kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a watan Azumin Ramalanan bara, gidauniyar Dangote cikin akidunta na bayar da tallafi ta rarraba kayayyakin abinci na kimanin Naira miliyan 300 zuwa ga akalla mutane 106,000 da ke jihohin Sakkwato, Katsina, Kebbi da kuma Zamfara.

A cikin jawabansu da suka gabatar daban-daban, Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Abubakar Sa'ad; Sarkin Argungu, Mai Martaba Alhaji Sama’ila Muhammad-Mera da kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, sun yabawa gidauniyar Dangote dangane da ayyukan jin kain talakawa da ta ke aiwatarwa, lamarin da suka misalta a matsayin dukiyar da ta yalwatu da riba.

KARANTA KUMA: Dalilan da ya sa Askarawa ke tsaron limamai a Masallacin Makkah

Ana iya tuna cewa, makonni kadan da suka gabata ne Dangote da ya bayar da gudunmawar dalar Amurka miliyan 20 ga wata cibiyar Afrika da ke kasar Amurka.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, cibiyar ita ce a kan gaba wajen mayar da hankali a kan jibintar al'amuran da suka shafi Afrika da gyara suna da tarihin nahiyar a idon duniya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel