Shugaba Buhari ya jinjinawa Dangote kan gudunmuwar N200m da ya bada don yakar Coronavirus

Shugaba Buhari ya jinjinawa Dangote kan gudunmuwar N200m da ya bada don yakar Coronavirus

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa gidauniyar hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, kan gudunwar makudan kudin da tayi alkawarin badawa domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki a ranar Laraba inda ya bayyana yadda ya kamata yan Najeriya suyi idan kasa na fuskantar kalubalae irin wannan.

Yace: "Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa gidauniyar Aliko Dangote Foundation (ADF) kan gudunmuwar N200m da ya bada wajen yakar cutar Coronavirus a kasa."

"Shugaba Buhari ya yi waiwaye kan yadda gidauniya ta taimaka da Bilyan daya wajen yakar cutar Ebola a baya."

Shugaba Buhari ya jinjinawa Dangote kan gudunmuwar N200m da ya bada don yakar Coronavirus
Dangote
Source: Getty Images

KU KARANTA: Coronavirus: An killace yan kasar Sin hudu a Abuja

Jiya mun kawo muku rahoton cewa Gidauniyar Alhaji Aliko Dangote (ADF) tayi alkawarin ba da gudunmuwar milyan dari niyu (N200m) domin taimakawa gwamnatin tarayya wajen takaita yaduwar cutar coronavirus a Najeriya.

Zuwaira Yusuf, Shugabar gidauniyar, a wani jawabi ranar Talata a Legas, ta bayyana cewa taimakon yana daya daga cikin muhimman manufofin gidauniyar.

Zuwaira tace gidauniyar ta tanadi N124m domin taimakawa asibitoci wurin gwaji, kula da kawar da cutar a hanyoyin shiga Najeriya domin tabbatar da lafiyar kasa baki daya.

A cewarta, gidauniyar zata samar da cibiyoyin bincike kan cutar na kimanin N36m domin taimakawa gwamnati.

Tace har ila yau, gidauniyar zata bada N48m domin kula da wadanda suka kamu da cutar da kuma horar da masu kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel