EndSARS: Mafi yawan 'yan sandan Najeriya nagari ne - IGP Adamu

EndSARS: Mafi yawan 'yan sandan Najeriya nagari ne - IGP Adamu

- Sifeta janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu, ya ce 'yan sanda mutanen kirki ne, ba kamar yadda ake yi musu bakin fenti ba

- Ya fadi hakan ne a hedkwatar 'yan sanda ta jihar Legas ranar Talata, bayan duba barnar da bata-gari suka yi

- Ya ce jajircewar 'yan sanda a lokacin da bata-gari suka yi ta kashe-kashe da lalata dukiyoyin gwamnati ne tabbacin zancensa

Muhammad Adamu, Sifeta janar na 'yan sanda, ya ce yawancin 'yan sanda mutanen kirki ne, ba kamar yadda suka yi kaurin suna sakamakon zalunci wanda ya janyo zanga-zangar EndSARS.

Ya fadi hakan ne a ranar Talata, lokacin da ya kai ziyara jihar Legas, don duba irin barna da aika-aikar da aka yi wa ofisoshin 'yan sanda a jihar.

Adamu ya sanar da kama mutane 1,590 da aka yi a fadin Najeriya, bisa zargin kai hari sakamakon zanga-zangar EndSARS, The Cable ta wallafa.

Yayi wannan maganar ne a hedkwatar 'yan sanda na jihar Legas, inda yace duk da farmakin da aka yi ta kai wa 'yan sanda, sun jajirce kuma sun danne zuciyoyinsu.

Ya ce a lokacin da bata-gari suka kai musu hari, lamarin yana da damar bata wa 'yan sanda rai har su kai ga harbinsu, amma 'yan sanda suka mayar da komai ba komai ba.

A cewarsa, "Mun nuna jajircewarmu wurin kwamtar da hankali da kin mayar musu da hari, yayin da bata-gari da 'yan ta'adda suka yi ta lalata kayan gwamnati da kashe-kashen rayuka."

KU KARANTA: Jarumi Adam A. Zango ya yi addu'a mai ratsa zuciya ga Rahama Sadau

Mafi yawan 'yan sandan Najeriya nagari ne - IGP Adamu
Mafi yawan 'yan sandan Najeriya nagari ne - IGP Adamu. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa muka ki komawa yajin aiki bayan wata 7 - ASUU

A wani labari na daban, Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce akwai yuwuwar 'yan daba ne suka saka kayan sojoji sannan suka dnga harbe-harbe a Lekki tollgate da ke jihar Legas.

Kusan makonni biyu da suka gabata ne matasa suka fara zanga-zanga inda suka bukaci a kawo karshen zaluncin 'yan sanda a fadin kasar nan.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi bukatar inda ya rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel