Mutum 10 sun mutu sakamakon trela da ta afka musu a kasuwa

Mutum 10 sun mutu sakamakon trela da ta afka musu a kasuwa

- Trela ta kubce wa direba ta faɗa cikin kasuwa ta kashe mutum 10

- Hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba a jihar Ondo

- Wadanda abin ya faru a idonsu sun ce birke ce ta dena aiki hakan yasa motar da ƙwace wa direban

Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Mutum 10 sun mutu sakamakon trela da ta afka musu a kasuwa
Mutum 10 sun mutu sakamakon trela da ta afka musu a kasuwa. Hoto: sunnewsonlne.com
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shaidun ganin ido sun bayyana cewa birkin trelan ne ya samu matsala

"Trelan na saukowa daga Dutsen Okerigo da ke kusa da Jami'ar Adekunle Ajasin ne a lokacin da ta kwace wa direban saboda rashin birki," a cewar majiyar.

Amma majiya daga rundunar ƴan sandan jihar ta ce mutum takwas ne suka mutu.

KU KARANTA: An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina

A wani labarin, kun ji an cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.

Fathi Hammad, shugaba a ƙungiyar Hamas daga Jabalia ya yi kira ga wadanda suka fito tattalin su hada kai don tunkaro abinda ya kira "cin zarafi" ga Annabi Muhammad.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel