2023: INEC ta fitar da N1bn, ta sanar da ranar cigaba da yi wa masu zabe rijista

2023: INEC ta fitar da N1bn, ta sanar da ranar cigaba da yi wa masu zabe rijista

- INEC ta sanar da lokacin da zata fara yi wa masu zabe rijista

- Za ta fara rijistar ne a watanni 4 na farko na 2021

- An ware naira biliyan 1 don yin rijistar masu zaben

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da lokacin da za ta cigaba da yin rijista ga masu (CVR) zabe, za su fara ne a watannin farko na 2021 saboda gabatowar zaben 2023.

An ware wa INEC naira biliyan 1 don yin CVR din, Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan ranar Laraba lokacin da ya gabatar da kasafin INEC ga majalisar dattawa.

Farfesa Yakubu ya nemi majalisar dattawa da ta amince da tayi amfani da naira biliyan 5.2 daga cikin kudaden da aka ware don cikasa kudin kasafin 2020 da ya gaza saboda cutar COVID-19.

Dama INEC ta dakatar da yi wa masu zabe rijista a watan Oktoba saboda annobar COVID-19.

KU KARANTA: Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau

2023: INEC ta fitar da N1bn, ta sanar da ranar cigaba da yi wa masu zabe rijista
2023: INEC ta fitar da N1bn, ta sanar da ranar cigaba da yi wa masu zabe rijista. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nsukka: Gwamnan Enugu ya bada umarnin gaggauta sake gina masallatai

A wani labari na daban, a jiya ne Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed yayi bayani a kan kashe naira miliyan 19 wurin tafiye-tafiye lokacin kullen COVID-19.

Ya sha 'yar kure a lokacin da ya je gaban kwamitin gabatar da kasafin ma'aikatarsa na 2021, Daily trust ta ruwaito.

Wani mamba na kwamitin kasafi, Ezenwa Onyewuchi ya ce masa: "Bari in tuna maka abubuwan da kace a kan kasafin 2020. An baka naira miliyan 30 don tafiye-tafiye cikin kasa, kace ka kashe naira miliyan 23, an baka naira miliyan 96, ka kashe naira miliyan 90.

"Batun tafiye-tafiyen kasashen ketare, an baka miliyan 43, ka kashe miliyan 19. Ina mamakin yadda ka iya fita kasashen ketare a lokacin kulle, wanda aka hana kowa fita kasashen waje, har da za kace ka kashe naira miliyan 19."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel