Nsukka: Gwamnan Enugu ya bada umarnin gaggauta sake gina masallatai

Nsukka: Gwamnan Enugu ya bada umarnin gaggauta sake gina masallatai

- Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ya bada umarnin kara gina masallatai 2 da 'yan zanga-zangar EndSARS suka rushe a jiharsa

- Gwamnan da ya samu wakilcin shugaban karamar hukumar Nsukka, Hon. Ugwueze, ya nuna alhininsa a kan faruwar lamarin

- Ya kuma jinjinawa musulmai a kan yadda ba su tayar da tarzoma ba bayan faruwar lamarin, ya ce lallai zai biya duk wanda asara ta sameshi

Shugaban karamar hukumar Nsukka, Hon. Ngwueze ya ce gwamnatin jihar Enugu ta yi alhini a kan yadda bata-gari suka rushe masallatai 2 da ke karamar hukumarsa, ya kai ziyara ta musamman jihar, inda ya tabbatar musu da cewa za'a fara aikin kara gina masallatan da aka rushe musu.

Mai girma gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya umarci a kara gina masallatai 2 da masu zanga-zanga suka rushe.

"Na zo ne don in tabbatar wa mutanen Enugu cewa gwamnati za ta biya duk wanda asara ta samesa sakamakon zanga-zangar EndSARS," yace.

Ya kuma yaba wa shugabannin musulmai a kan hakurin da suka yi a lokacin da rigimar nan ta hargitse a jihar.

"Na yaba wa shugabannin musulmai a kan yadda suka kwantar da hankulansu kuma ba su kai wa kowa farmaki ba bayan rushe masallatan da aka yi musu," cewarsa.

Yakubu Omeh, limamin babban masallacin Nsukka yayi godiya ga shugaban karamar hukumar a kan kawo musu ziyara da kuma tabbatar musu da alkawarin gwamna a kan kara gina masallatan da yayi.

Ya ce don an rushe musu masallatai ba za su kai wa wani mazaunin karamar hukumar Nsukka hari ba, duk da bambancin addini.

"Za mu yi iyakar kokarinmu wurin ganin mun tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin mutane masu bambancin kabilu da addinai."

Ya ce tsawon shekaru suna zaune lafiya da 'yan uwansu maza da mata, Vanguard ta wallafa.

Ya kuma nuna farincikinsa da ziyarar, don hakan ya nuna gwamnan ya nuna kulawa da kaunarsa ga musulman Nsukka.

Ya kara bayyana yadda suka tabbatar da zaman lafiya a yankin, inda ya ce yanzu haka hausawa da musulman Nsukka sun cigaba da rayuwarsu kamar kullum.

KU KARANTA: Bidiyon mutumin da aka hako yana numfashi bayan shekara daya da birne shi

Nsukka: Gwamnan Enugu ya bada umarnin gaggauta sake gina masallatai
Nsukka: Gwamnan Enugu ya bada umarnin gaggauta sake gina masallatai. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jarabarsa tayi yawa, a taimaka min a raba mu - Matar aure a gaban kotu

A wani labari na daban, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana yadda shugaba kasa Muhammadu Buhari yake kokarin samar wa matasa ayyukan yi, wanda ba a taba yin hakan ba a tarihin Najeriya.

A wani taron da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jagoranta a Kaduna, wanda shugabanni da manyan mutane da dama suka samu damar halarta, Mohammed ya sanar da shirin da shugaban kasar ya fara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: