Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau

Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau

- Shugaban kwamitin shirye-shiryen nadin sarautar Zazzau ya bayar da sanarwa ta musamman

- Ya sanar da ranar Litinin 19 ga watan Nuwamban 2020 a matsayin ranar da za a yi bikin nadin sarautar Zazzau

- Ana sa ran gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ne zai zama babban bako a wurin bikin

Wata sanarwa ta fita, wacce take kunshe da ranar da za a yi bikin nadin sarautar sabon sarki, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.

A ranar Litinin ne shugaban kwamitin shirye-shiryen nadin sarautar Zazzau suka sanar da ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamban 2020 ya zama ranar da za a yi nadin.

Za a yi nadin ne a filin wasan Polo da ke GRA, karkashin unguwar sabon gari a birnin Zariy\a.

An sanar da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai zai zama babban bako a wajen nadin.

Sannan akwai manyan baki da ake sa ran za su halarci wurin kamar ministoci, mambobin majalisar jiha da na dokoki, manyan 'yan siyasa, manyan 'yan kasuwa da kuma manyan ma'aikatan gwamnati da ke fadin Najeriya.

A ranar 19 ga watan Nuwamba ne ake sa ran nada Ambasada Ahmed Bamalli a matsayin sarkin Zazzau, bayan kasuwar sarki Shehu Idris.

KU KARANTA: Mbaka ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya hakuri a kan mulkin kama karya

Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Babu gwamnatin da ta fattaki talauci kamar ta Buhari - Lai Mohammed

A wani labari na daban, wani al'amari mai firgitawa ya faru a Umuoji, Amucha da ke jihar Imo, inda aka ga wani mutum da ya rasu shekarar da ta gabata yana numfashi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, a bidiyon, mutane sun taru a kan akwatin gawa, inda aka ga mutumin yana numfashi. Mutanen sun yi ta ihu suna cewa "yana numfashi, yana numfashi" cike da mamaki.

Kamar yadda labarin yazo, mutumin ya mutu ne ranar 9 ga watan Nuwamba, 2019 kuma an rufeshi ranar 8 ga watan Oktoban 2020, kamar yadda aka ji wani yana fadi a bidiyon.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng