Sabon bidiyon Shekau: Karamin yaro rike da bindiga yana barazanar tabbatar da tashin hankali

Sabon bidiyon Shekau: Karamin yaro rike da bindiga yana barazanar tabbatar da tashin hankali

- Sojoji sun samu wani bidiyo na 'yan Boko Haram bayan kashe 'yan ta'addan guda 75 a Borno

- Bidiyon ya kunshi wani yaro ne mai sanye da kayan sojoji yana furta kalaman tsana ga duk wanda ba dan Boko Haram ba

- Yaron mai rike da bindiga yace "babu gudu babu ja da baya, ko dai ku yi imani ko mu kashe ku"

'Yan ta'addan Boko Haram, karkashin jagorancin Abubakar Shekau sun saki wani sabon bidiyo wanda yake nuna wani yaro da kayan sojoji yana nuna ta'addancinsa a fili a ranar Talata.

Bidiyon da 'yan ta'addan suka saki ya nuna yaron mai sanye da kayan sojoji rike da makami, HumAngle ta ruwaito.

Bidiyon na mintina 5 mai taken "Alwala'a Wal Bara'a", inda suke nuna tsananin kiyayya da yaki ga duk wanda ya shiga tarkonsu.

"Hakika babu gudu ba ja da baya. Muna da banbancin da ku. Ko dai ku tuba ko kuma mu kashe ku," Kamar yadda aka ji karamin yaron wanda ya ke rike da bindiga yana fadi.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, 'yan Boko Haram sun horar da yara kanana, wadanda za su kai 1,385 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019, don cigaba da ta'addanci.

Kungiyar tana amfani da yara wadanda suka sace ko kuma marayu don kone-kone a garuruwa.

A ranar 24 ga watan Disamban 2014, an kama wata Zahra'u Babangida a arewa maso yamman Najeriya tana kokarin fasa wani abu mai fashewa wanda aka daure a jikinta.

An kama yarinyar da sati 2, wasu yara mata 2 suka fasa abu mai fashewa a kasuwa, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 10.

An ji muryar Abubakar Shekau a karshen bidiyon, inda yake cewa kungiyarsu ta tsani duk wanda ba dan Boko Haram bane.

Kuma Wallahi babu wanda zai ga fuskarsu har sai yayi imani da Ubangiji.

An samu bidiyon ne a hannun sojoji bayan sun kashe 'yan Boko Haram 75 a fadan karshe da suka yi da su.

KU KARANTA: Da duminsa: An saka ranar shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau

Sabon bidiyon Shekau: Karamin yaro rike da bindiga yana barazanar tabbatar da tashin hankali
Sabon bidiyon Shekau: Karamin yaro rike da bindiga yana barazanar tabbatar da tashin hankali. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsaro da satar kayan tallafi: Gwamnonin Najeriya za su yi muhimmin taro

A wani labari na daban, wani bidiyo mai narkar da zuciya yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda aka ga wata mata bahaushiya wacce tayi shekaru 25 a jihar Enugu tana hira da wani dan kudu maso gabas da yaren Ibo.

Matar wacce ba'a gano sunanta ba ta zauna a Enugu na tsawon shekaru 25, inda aka ji mutumin yana jefa mata tambayoyi da yaren, ita kuma tana maida masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: