Bidiyon dattijuwa daga Sokoto tana magana da yaren Ibo tiryan-tiryan babu kuskure

Bidiyon dattijuwa daga Sokoto tana magana da yaren Ibo tiryan-tiryan babu kuskure

- Ya kamata a ce 'yan Najeriya sun cigaba da nuna wa juna soyayya da hadin kai ba tare da duba banbancin addini ko kabila ba

- Wani bidiyo ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda aka ga wata mata mai hijabi 'yar asalin jihar Sokoto tana hira da wani dan kabilar Ibo da yarensa

- Wannan bidiyon ya janyo hankalin mutane da dama, inda aka yi ta tsokaci masu ban sha'awa a kan matar da tayi shekaru 25 a jihar Enugu

Wani bidiyo mai narkar da zuciya yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda aka ga wata mata bahaushiya wacce tayi shekaru 25 a jihar Enugu tana hira da wani dan kudu maso gabas da yaren Ibo.

Matar wacce ba'a gano sunanta ba ta zauna a Enugu na tsawon shekaru 25, inda aka ji mutumin yana jefa mata tambayoyi da yaren, ita kuma tana maida masa.

Wannan bidiyon ya nuna hadin kai da soyayya tsakanin 'yan Najeriya. Matar, 'yar asalin jihar Sokoto ta burge mutane da dama ta yadda take sarrafa harshenta tana yin yaren Ibo cikin kwarewa.

Wannan bidiyon ya sa mutane da dama suna tsokaci iri-iri, ga wasu daga ciki:

Wani Kayode cewa yayi: "Wadanda basu zagaya Najeriya bane kadai za ka ji suna cewa a raba kasar nan ba tare da tunanin 'yan uwansu da ke Potiskum, Mongunno, Azare, Okigwe, Badagry da sauran su ba. Munanan tare, kuma za mu canja kasar nan da taimakon junanmu."

Wani maabdul cewa yayi: "Wannan shine asalin hadin kai, haka kuma yakamata Najeriya ta zama, babu bambancin addini, kabila ko kuma asali. Amma muna nan muna zagin juna maimakon nuna soyayya da hadin kai ga juna."

Da sauran tsokaci iri-iri daga mutane daban-daban dake fadin Najeriya.

KU KARANTA: Da duminsa: EFCC ta yi wa tsohon shugaban FIRS kiran gaggawa

Bidiyon dattijuwa daga Sokoto tana magana da yaren Ibo tiryan-tiryan babu kuskure
Bidiyon dattijuwa daga Sokoto tana magana da yaren Ibo tiryan-tiryan babu kuskure. Hoto daga @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 170 sun harbu da korona a Najeriya

A wani labari na daban, dangin fursunoni 1,181 daga cin wadanda suka gudu daga gidajen gyaran hali na Oko da Benin sun maido dasu da kansu, jaridar Leadership ta wallafa hakan.

Wata majiya daga gidan gyaran halin ta tabbatar da cewa 'yan uwan mutane 24 daga cikin wadanda suka gudu sun dawo dasu tare da lauyoyinsu a ranar 30 ga watan Oktoba, 2020, a bisa umarnin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel