Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Muhammad Adahama

Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Muhammad Adahama

- Buhari ya bayyana mamacin a matsayin wanda ya taimaka masa a harkokin siyasa

- Ya bayyana shi a matsayin gogaggen malami kuma mai son fadar gaskiya

- Ya kuma mika ta'aziyyar limamin masallacin Uthman bin Affan a Abuja

Shugaban Muhammadu Buhari ya bayyana alhinin sa game da rasuwar wani jigo a Kano kuma mashahurin malami Muhammad Adahama, inda ya bayyana shi a matsayin "abokin da suka dade, kuma mashahurin gogaggen malami."

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Garba Shehu, a Abuja ranar Litinin, Buhari ya yabi marigayi Khalifa daga tsatson Adahama a birnin Kano, wanda ya bayyana cewa ya tsaya masa kan al'amuran siyasarsa a duk lokacin da yake fafutukar siyasar.

Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Muhammad Adahama
Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Muhammad Adahama. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A cewarsa, labarin siyasar Muhammadu Buhari ba zai kammala ba, ba tare da an ambaci irin ƙoƙarin irin su Adahama ba kamar yadda The Punch ta ruwaito.

"A madadina da iyalaina, gwamnati da al'ummar Najeriya, ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalai da abokan mamacin, da kuma gwamnati da al'ummar kano," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

Mamacin Kaka ne a wajen babban mai taimakawa Shugaba Buhari bangaren matasa, Nasiru Adahama.

Shugaban ya kuma bi dubban musulmi wajen mika ta'aziyyar Abduljalil Dabo, a babban birnin tarayya Abuja, Babban limamin masallacin Uthman bin Affan, da ke kallon Banex/Emab plaza, Wuse 2, Abuja.

A sakon da ya turawa iyalan mamacin da kuma mabiyan malamin addinin Buhari ya bayyana shi a matsayin adalin shugaba, mara tsoron da kuma karfin gwiwar fadar gaskiya.

Shugaban wadda ya samu wakilcin Dakta Isah Ali Pantami a wajen jana'izar malamin ya ce, "mutanen Abuja sun rasa malami kuma mai bada tarbiyya, kuma musulmi a ƙasar sun rasa shugaba mai inganci. Muna addu'ar Allah ya bada ladan ayyukan da yayi."

KU KARANTA: Kannywood ta kori Rahama Sadau, ta bukaci sauran jarumai da su yanke alaka da ita

A wani labarin, Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel