Da duminsa: Da sauran sakamakon jihohi 6, Trump ya lashi takobin garzayawa kotu
- Donald Trump ya mika godiyarsa ga al'umma bisa goyon bayan da suka bashi
- Shugaban kasan ya jaddada imanin cewa shi ke hanyar nasara a zaben
- Idan trump ya fadi zaben nan, zai zama shugaban kasa na 11 a tarihi da zai fadi zabe
Shugaba Donald Trump a ranar Laraba ya yi ikirarin cewa ya lashe zaben kujerar shugaban kasa, duk da cewa ba'a kammala fitar da sakamako ba, kamar yadda muka gano a bidiyon Aljazeera.
Hakazalika Trump ya lashi takobin garzayawa kotun koli domin dakatad da kirgan sauran kuri'u.
"Mun lashe zaben," Trump yace a jawabin da yayi da safiyar Laraba a fadar White House.
"Domin alherin kasar nan, wannan lokaci ne mai muhimmanci. Wannan magudi ne babba a kasarmu. Muna son ayi amfani da doka yadda ya kamata. Saboda haka, zamu garzaya kotun koli," Trump ya kara.
A yadda sakamakon yake yanzu, Trump na bayyana abokin hamayyarsa Biden kuma ya ce yana bukatar a tsayar kirgan kuri'u.
KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 213, Biden 238
KU KARANTA: Zaben Amurka: An saka dokar ta baci a jihar Oregon
Mun kawo muku cewa Donald Trump ya na zargin cewa ana kokarin sace masa kuri’u. Shugaban kasar bai bada wasu hujjoji da za su gaskata ikirarin da ya ke yi ba.
Shugaban ya ce an kyale wasu su na kada kuri’a a lokacin da ya kamata ace an rufe rumfuna.
Trump ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter, Legit.ng ta fahimci cewa Twitter ta yi wa wannan magana tambarin kanshin rashin gaskiya.
“Mu na gaba, amma su na kokarin sace zaben. Ba za mu taba bari su yi wannan ba.” Inji Trump.
“Ba za a rika kada kuri’a bayan an rufe rumfunan zabe ba.”
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng