Dalilin da yasa muka ki komawa yajin aiki bayan wata 7 - ASUU

Dalilin da yasa muka ki komawa yajin aiki bayan wata 7 - ASUU

- ASUU ta yi bayani a kan dalilinta na kin komawa yajin aikin da ya kwashe watanni bakwai

- Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da rashin gaskiya, tsoratarwa da kuma hada karairayi

- Kamar yadda suka bayyana, gwamnatin tarayyar bata cike alkawurranta ba tun na 2009

Kungiyar malaman jami'o'i ta yi bayanin dalilin da yasa yajin aikinta na tsawon watanni uku ya kasa ci balle cinyewa, duk da jerin taron da suka dinga da gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya, ta ce hakan ya zarce har ya koma tsoratarwa tare da hada karya ga jama'a a maimakon yin kokarin ganin karshen yajin aiki.

Kungiyar ta yi bayanin ne a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin ta hannun shugabanta na reshen jihar legas, kuma ta samu sa hannun Olusiji Sowande, Premium Time ta wallafa.

Kamar yadda takardar tace, lamarin ya fara ne da gazawar gwamnati wurin cika alkawarin ta na 2009 wanda suka hada da gyaran lalatattun ababen more rayuwa da suka hada da dakunan kwana, dakunan daukar karatu, dakunan gwaje-gaje da sauransu.

"Hakan ya hada da biyan kudin alawus, kafa kwamitin ziyara domin duba yanayin ayyuka da shugabancin jami'o'i," Sowande yace.

KU KARANTA: A dawo mana da mazakutarmu: Hotunan fusatattun matasa suna zanga-zanga a Benue

Dalilin da yasa muka ki komawa yajin aiki bayan wata 7 - ASUU
Dalilin da yasa muka ki komawa yajin aiki bayan wata 7 - ASUU. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni

A wani labari na daban, a ranar Lahadi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa game da harin da jami'an tsaro suka kai wa masu zanga-zangar lumana a jihohin Najeriya.

Wannan furucin na shugaban kasa ya biyo bayan labaran da suka yi ta yawo a sati biyu da suka gabata, inda ya nuna fushinsa a kan harin da jami'an tsaro suka kai wa masu zanga-zangar lumana na EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng