EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai

EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kwatanta halaka 'yan sanda da babban abun Allah wadai

- Kamar yadda gwamnan ya sanar da manema labarai a garin Kaduna, a kowanne aiki akwai wadanda ba nagari ba

- Ya jaddada cewa za su dage wurin inganta aikin 'yan sandan amma kashesu ba wata hujja bace

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Litinin ya kwatanta kashe-kashen 'yan sanda da masu zanga-zanga ke yi a wasu sassan kasar nan a matsayin babban abun ashsha.

El-Rufai, wanda ya zanta da manema labarai a Kaduna bayan taron zauren gwamnonin arewa da masu sarautar gargajiya tare da sauran masu ruwa da tsaki a yankin, ya ce dole ne a goyi bayan 'yan sandan idan ana so su dinga sauke nauyinsu.

Ya ce sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya yi masu bayani dalla-dalla a yayin taron, The Punch ta wallafa.

Gwamnan ya ce, "Ina goyon bayan 'yan sanda, mun yadda cewa akwai wadanda ba nagari ba a cikin kowanne wuri, amma wannan ba hujja bace ta kashesu.

"Muna fatan fadadawa tare da inganta aikin 'yan sanda a Najeriya. Mun tattauna da IGP da kuma gwamnoni ta yadda za mu inganta aikin."

KU KARANTA: Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni

EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai
EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: A dawo mana da mazakutarmu: Hotunan fusatattun matasa suna zanga-zanga a Benue

A wani labari na daban, Gwamna Obaseki na jihar Edo ya yi kira ga 'yan sanda da su koma bakin aikinsu. Bayan rikicin da ya barke ta sanadin zanga-zangar EndSARS, 'yan sanda sun bar ayyukansu a fadin jihar, lamarin da ya kawo rashin doka da oda.

A yayin rikicin, an kai wa ofisoshin 'yan sanda hari tare da balle gidajen gyaran hali na Benin da Oko inda aka sako masu zaman gidan har 1,993, The cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng