OPWS: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun kwace miyagun makamai da kwayoyi
- Zakakuran sojin Najeriya na cigaba da samun manyan nasarori a fannin yakar 'yan ta'adda a fadin kasar nan
- Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo janar John Enenche ya sanar, sun kashe 'yan bindiga 2 a Benue
- Ya ce sauran sun tsere da miyagun raunika sannan sun samu miyagun makamai da kwayoyi a wurinsu
Rundunar soji ta Operation Whirl Stroke ta samu nasarar halaka wasu 'yan bindiga, kwato miyagun makamai da kuma wasu kwayoyi a jihar Benue.
A sakamakon cigaban kokarin dakarun sojin Najeriya na ganin bayan 'yan bindiga da sauran miyagun al'amura a fadin kasar nan, rundunar Operation Whirl Stroke ta halaka 'yan bindiga biyu a jihar Nasarawa.
Rundunar hadin guiwa ta fita sintiri a ranar 18 ga watan Oktoban 2020 a kauyukan Kango da Adumata inda ta tarar da wasu 'yan bindiga.
Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar John Enenche ya sanar, zakakuran sojojin sun yi aragangama inda suka yi musayar wuta.
Daga nan suka fi karfin 'yan binidgan inda suka kashe biyu daga ciki sannan wasu suka tsere da miyagun raunika.
Dakarun sojin sun samu bindiga daya kirar AK47, bindigar toka daya, carbin harsasan AK 47 shida da kuma miyagun kwayoyi.
Rundunar sojin Najeriyan tare da sauran jami'an tsaro sun dauka alkawarin cigaba da samar da zaman lafiya tare da tsaro a fadin kasar nan.
KU KARANTA: EndSARS: Ministan tsaro ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga masu zanga-zanga Read more:
KU KARANTA: Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya
A wani labari na daban, Dama dakataccen shugaban EFCC na fuskantar kwamitin bincike bisa zargin da ake yi masa na amfani da ofishinsa ta hanyar da bai dace ba, da watanda da dukiyar gwamnatin tarayya daga watan Mayu 2015 zuwa 2020.
Antoni janar, Abubakar Malami, ya mika takardar zargin Magu zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng