Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone 11 da ya siya mata

Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone 11 da ya siya mata

- Wani matashi mai suna Busdor ya bayar da labarin yadda ta kaya tsakanin wani mutum mai aure da budurwarsa

- Saurayin ya ce mutumin ya kama budurwar tasa da wani saurayi daban, sai ya kwace wayar da ya siya mata

- Ita kuma budurwar ta kira masa 'yan sanda, amma ya ki ba su dama, yace ta rike duk abinda ya siya mata amma banda wayar

Wani saurayi mai suna Busdor ya bayar da labarin al'amarin da ya faru tsakanin wani mutum mai aure da matarsa ta ke Ingila, da budurwarsa wacce makwabciyar Busdor ce.

A cewarsa, mutumin ya ziyarci budurwarsa ne sai ya same ta tare da wani saurayin, take a nan ya kwace wayar da ya siya mata.

Bayan motarsa ta samu matsala kusa da gidan budurwar, washegari da safe ta kira masa 'yan sanda don su amso mata wayarta. Mutumin kuwa ya ki bude kofa, a cewarsa yana tare da kananan yaransa kuma tsoro suke ji.

Ya ce budurwar ta rike gida da shagon da ya siya mata, amma ba zai bayar da wayar ba.

KU KARANTA: Ba na goyon bayan kai wa masu zanga-zanga hari - Buhari ga matasa

Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone da ya siya mata
Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone da ya siya mata. Hoto daga @busdor101
Asali: Twitter

KU KARANTA: WAEC: Adadin wadanda suka samu nasara da yawan wadanda aka rike wa sakamako

A wani labari na daban, Samarin unguwar Daudu da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, sun fara zanga-zangar a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, a kan batan mazakutarsu a cikin kauyen.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, samari 7 kenan a kauyen suka duba mazakutarsu suka ga tayi layar zana. Wani matashi ya kashe kansa a ranar 11 ga watan Oktoba, bayan an zargesa da sace mazakutar wani.

Sun fara zanga-zangar a kasuwar Daudu, sakamakon haka titin Makurdi zuwa Lafiya ya cunkushe kafin isowar 'yan sanda, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng