'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron

'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron

- Ƴan kungiyar Shi'a ta IMN sun gudanar da zanga zangar nuna fushi ga Shugaban Faransa Emmanuel Macron

- Mambobin Ƙungiyar sunyi zanga-zangar ne a birnin tarayya Abuja inda suka ƙona tutar Faransa

- Masu zanga-zangar sun yi tir da kalaman Shugaba Macron inda suka ce sun ƙona tutar ƙasarsa ne don nuna fushinsu kan harin da suka ce yana yi wa musulmi da musulunci

Mambobin Ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da aka fi sani da Shi'a, a ranar Talata 3 ga watan Nuwamba sun ƙona tutar kasar Faransa a Abuja kan kalaman "rashin son musulunci" da aka danganta da Shugaba Emmanuel Macron.

Idan za a iya tunawa ƙasashen musulmi da dama sun nuna fushinsu kan yadda gwamnati Faransa game da ɓattancin da aka yi wa Annabi Muhammad SAW.

A bangarensa, Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi jinjina ga Samuel Paty, malamin da aka kashe a ranar 16 ga watan Oktoban 2020.

'Yan Shi'a sun kona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron
'Yan Shi'a sun kona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron. Hoto: @linda_ikeji
Asali: Twitter

An kai wa Paty hari ne a kusa da makarantar sa da ke kusa da Paris saboda nuna wa ɗalibai zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad.

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

Ƴan sanda sun bindige wanda ya kashe shi, Abdullakh Anzorov, mai shekaru 18 har lahira.

A jawabin da ya yi a talabijin a ranar 28 ga watan Oktoba, Mista Macron ya shaidawa masu kallo cewa Faransa "ba za ta dena yin zanen barkwancinta ba".

A cewar BBC, Macron ya ce Mista Paty ya yi kokarin koyar da ɗalibansa yadda za su zama ƴan ƙasa ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Macron ya kuma kare ikon 'furta ɓatanci' a ƙarƙashin ƴancin furta albarkacin baki a watan Satumba kuma ya ce akwai bukatar a yi wa musulunci 'garambawul' don ya dace da tsarin ƙasar.

A yayin tattakin su da suka kammala a kasuwar Wuse, ƙungiyoyin IMN sun ƙona tutar Faransa yayin da suke rera waƙoƙi. Wani ɗan ƙungiyar, Sidi Munir ya kwatanta jaridar a matsayin hari ga musulmi.

KU KARANTA: An yi jana'izar jakadar Najeriya a Jordan, Haruna Ungogo a Kano

Munir ya ce;

"Mun ƙona tutar Faransa ne a matsayin martani kan harin da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai musulunci da musulmi tun bayan aikata babban laifi na wallafa zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad da mujallar Charlie Hebdo ta yi.

"Don haka muna goyon bayan zanga zangar da musulmi da dukkan masu son zaman lafiya da lumana ke yi."

A wani labarin, Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164