An yi jana'izar jakadar Najeriya a Jordan, Haruna Ungogo a Kano

An yi jana'izar jakadar Najeriya a Jordan, Haruna Ungogo a Kano

- An birne marigayi Alhaji Haruna Ungogo a maƙabartar Na'ibawa da ke Kano a ranar Litinin

- Marigayin jakadar ta Najeriya a ƙasar Jordan ya rasu ne a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja

- Haruna Ungogo ya rasu ne bayan gajeruwar jinya da ya yi a asibitin na Abuja

An birne gawar tsohon jakadar Najeriya a ƙasar Jordan, Alhaji Haruna Ungogo a maƙabartar Na'ibawa Gabas da ke birnin Kano misalin ƙarfe 9.59 na safiyar ranar Litinin.

Marigayin jakadar ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi a asibitin babban birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An yi jana'izar jakadar Najeriya a Jordan, Haruna Ungogo a Kano
Alhaji Haruna Ungogo. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Kungiya ta yi barazanar yin ƙarar El-Rufai a kotu idan ya ki fitowa takarar shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi jakada a masarautar Jordan da kuma Jamhuriyar Iran a shekarar 2016 har zuwa lokacin da ya rasu.

Ungogo ya kuma yi aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya kuma taɓa rike muƙamin kwamishinan Kudi a Jihar.

KU KARANTA: Mutum 10 sun mutu sakamakon trela da ta afka musu a kasuwa

Kazalika, marigayi Ungogo ya taɓa rike muƙamin shugaban kwalejin kimiyya ta jihar Kano wato Kano State Polytechnic.

A wani labarin, kun ji an cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.

Fathi Hammad, shugaba a ƙungiyar Hamas daga Jabalia ya yi kira ga wadanda suka fito tattalin su hada kai don tunkaro abinda ya kira "cin zarafi" ga Annabi Muhammad.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel