Bidiyon mutumin da aka hako yana numfashi bayan shekara daya da birne shi

Bidiyon mutumin da aka hako yana numfashi bayan shekara daya da birne shi

- Wani al'amari mai ban mamaki ya faru a jihar Imo, inda aka ga gawa tana numfashi

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, gawar da ta shekara 1 a kwance aka gani tana numfashi

- An ga yadda kwari suka fara cin akwatin gawar, amma jikin mamacin bai rube ba

Wani al'amari mai firgitawa ya faru a Umuoji, Amucha da ke jihar Imo, inda aka ga wani mutum da ya rasu shekarar da ta gabata yana numfashi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, a bidiyon, mutane sun taru a kan akwatin gawa, inda aka ga mutumin yana numfashi.

Mutanen sun yi ta ihu suna cewa "yana numfashi, yana numfashi" cike da mamaki.

Kamar yadda labarin yazo, mutumin ya mutu ne ranar 9 ga watan Nuwamba, 2019 kuma an rufeshi ranar 8 ga watan Oktoban 2020, kamar yadda aka ji wani yana fadi a bidiyon.

An ji muryar wani mutum yana cewa, "mutumin nan ya mutu a shekarar da ta gabata da sati 3 kenan da birne shi, sai ga shi yana numfashi."

Wani kuma ya ce an rufe mutumin tun shekarar da ta gabata.

An ji wani daga gefe yana cewa "tun da nake, ban taba ganin irin wannan al'amarin ba."

Yace an birne gawar mutumin ne a wurin ba nashi bane.

Kamar yadda aka gani, kwari sun fara cin akwatin gawar amma gawar bata rube ba ko kadan.

Daga baya an kira diyar mamacin, inda aka nuna mata shi ko za ta gane mahaifinta.

KU KARANTA: Ahmad Bamalli: Kotu ta saka ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau

Bidiyon mutumin da aka hako yana numfashi bayan shekara daya da birne shi
Bidiyon mutumin da aka hako yana numfashi bayan shekara daya da birne shi. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon dattijuwa daga Sokoto tana magana da yaren Ibo tiryan-tiryan babu kuskure

A wani labari na daban, wani dan shekara 40 mai suna Etifa Obukulubu, ya banka wa gidan da ke wuraren igbogene, karamar hukumar Yenagoa, wuta a ranar Asabar saboda zargin budurwarsa tana tarayya da wani.

Sakamakon wutar, wani fasto da ke aiki da sabuwar cocin Baptist da wata yarinya sun kone har lahira.

Kamar yadda aka tattaro bayanai, al'amarin ya faru ne da karfe 3:00 na daren ranar Lahadi, wanda jama'a suka yi ta kokarin kashe wutar amma abin yaci tura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng